4 Afirilu 2026 - 10:46
Source: ABNA24
Iran Ta Rataye Ƴan Ta'adda Biyu A Yau 

An rataye wasu mambobi biyu na tawagar 'yan ta'addan a Tehran bayan bin matakan shari'a da tabbatar da laifukan ta'addancinsu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Abolhassan Montazer da Wahid Bani-Amarian wasu 'yan ta'adda ne na kungiyar ta'addancin munafikin a Tehran da ke gudanar da ayyukan ta'addanci bisa umarnin maƙiya. Wanda ya ke bayan shari'a da tabbatar da hukuncin a Kotun Koli. Mambobin wannan tawaga mai dauke da makamai na munafukai sun gudanar da ayyukan ta'addanci da fashe-fashe da dama a karkashin jagorancin abokan gaba a Tehran. 

Abolhassan Montazer, ɗan Seyed Jafar, shi da Mohammad Taghavi dayan shi ma da aka rataye shi sun taka muhimmiyar rawa mai tasiri wajen jagorantar ƙungiyar; ta yin amfani da kasafin kudin da munafukai suka ba su, sun samar da wani gida mai tsaro don gudanar da ayyukan kungiyar tare da samarwa da sauran mutanensu gidajen haya. 

Dangane da abin da ke cikin shari'ar, an gano wasu ayyukansu na ta'addnci da na'urorin harba ababen fashewa. 

Abolhassan Montazer ya kasance memba na kungiyar ta'addanci na munafukai, wanda ya aiwatar da ayyukan farfaganda da cutarwa ga al'umma tare da hadin gwiwar sauran mambobin kungiyar, sun aiwatar da ayyukan makamai bisa tsarin manufofin kungiyar. Ya kasance yana samar da gidan hayar tawagar yana biyan haya da adadin kuɗin da aka ba shi ta hanyar crypto. 

Sun kuma yi amfani da gidajen hayar wajen kera makamai da na'urorin harba ababen fashewa. 

Wahid Bani Amerian, dan Mohammad, ya kasance wani memba na kungiyar munafukai a wannan harka, wanda, tare da Abolhassan Montazer, an kama su yayin da suke yunkurin harba makamai hudu. Ya kuma kasance daya daga cikin 'yan kungiyar ta'addanci na munafukai, wadanda bayan sun sake haduwa da kungiyar, sun fara aiwatar da farfaganda da cutarwa ga al'umma daidai da manufofin kungiyar. Har ila yau wanda aka yanke wa hukuncin ya yi tarayya wajen kai hare-hare a wurare daban-daban. Ya dade yana boye kuma yana siyan sabbin wayoyin hannu da katunan SIM don tuntubar shugabannin su ta Telegram. 

Bayan kamawa da shigar da karar, Abolhassan Montazer, dan Jafar da Wahid Bani Amerian, dan Mohammad, bisa zargin ayyukan ta'addanci daban-daban da fashe-fashe karkashin kungiyar ta'addanci ta munafukai. Kotun, bayan gudanar da bincike kan karar da kuma samun kariyar wadanda ake kara da lauyoyinsu, a cewar rahoton jami’an, An kai ga tabbatar da laifukan su an kuma yanke masu hukuncin kisa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha