18 Maris 2026 - 15:20
Source: ABNA24
Yanzu-Yanzu: Hare-Hare Hadin Gwiwar Isra’ila Da Larabawa Da Amurka A Kan Cibiyar Petrochemical A Assaluyeh Bushehr

Hadin Gwiwar jiragen yakin AMurka da Isra’ila da Kasashen Larabawa sun kai hari kan yankuna da dama cibiyar tace mai da suka hada da yanki na 15, 16, 17, 18 a Kudancin Pars a Assaluyeh.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Bayan da Trump yayi tir da rashin  hadin gwiwar kasashen NATO da Turai kan yakar Iran, amma sai ga UAE, Qatar da Saudi Arabia sun goya masa baya inda suka kai hari a cibiyar tace mai ta Pars Petrochemical da ke Kudancin Pars Assaloyeh da ke Bushehr sun kai hari kan ɓangaren daban-daban na cibiyar. Har yanzu ba a tantance ainihin bayanan sakamakon harin ba.

Amma Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce, bayan wannan harin Iran ta harba makamai masu linzami 13 da wasu jirage marasa matuka 27 na kunar bakin wake a sansanin Amurka da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha