18 Maris 2026 - 14:49
Source: ABNA24
Iran Tai Kai Hari Wurin Da Isra’ila Ke Ajiye Jiragen Saman Yaki Masu Daukar Mai

Iran ta kai hari kan wuri mai muhimmanci na sojojin sahyoniyawa gurin da su ke amfani da shi wajen ajiye manyan jiragen yaki masu dukar mai da domin karawa jiragen yain Isra’ila mai yayin da suke aki hari wani wuri

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Iran ta ki hari mai tsanani da jiragen marasa matuka na sojojinta kan matattarar jiragen yakin Isra’ila da jiragen tankokin dakon man fetur da suke a filin jirgin saman Ben Gurion wanda wadannan jirage suna taka muhimmiyar rawa wajen kai harin ta'addanci a kan kasar Iran da fagen gwagwarmaya.

Ofishin hulda da jama'a ta rundunar ta sanar a cikin sanarwar mai lamba 33: Tun daga safiyar yau, a ayyukan ramuwar gayya ga tsarkakakken jinin jaruman shahidai na jirgin Dena da jinin Dakta Ali Larijani da Manjo Janar Gholamreza Soleimani, mun gudanar da kai da hare-hare jirage marasa matuki kan wurin da jiragen saman gwamnatin Sahayoniyya ke jibge a filin jirgin saman Ben Gurion.

A cikin wannan sanarwar, sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yayin da suke yabawa da jinjinawa bisa halartar yawan jama'a cikin jarumta a taron bankwana da shahidan Dena, sun kira wannan halartar da hadin kai da yake a matsayin ginshiki na karfafa ruhin sojojin tare da jaddada cewa: Zasu ci gaba da ayyukan ramuwar gayya ga abokan gaba na Amurka da Isra’ila da dukkan iyawarsu.

Jiragen yakin sojojin saman Isra'ila da tankokin dakon mai da suke jibge a filin jirgin saman Ben Gurion sun taka muhimmiyar rawa wajen ta'addanci kai tsaye da tallafawa hare-haren jiragen sama a kan kasar Iran da fagen gwagwarmaya.

....................................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha