17 Maris 2026 - 17:47
Source: ABNA24
Iran: An Kama Sojojin Hayar Amurka Da 62

Ma'aikatar Leken Asiri: An kama ɗaruruwan na'urar Starlink da makiya Amurka-Israila suka aiko zuwa Iran tare da kama sojojin hayarsu guda 55

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar leken asiri ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Sojojin Imam Zaman AF cikin wasu jerin ayyuka masu yawa bisa amfani da na'urorin fasaha sun gano dukkan tashoshin intanet na tauraron dan adam da ke hidima ga abokan gaba tare da sarrafasu. 

Waɗannan yunkurori ba zasu takaita ba har sai an kama tare da gano dukkan waɗannan na'urorim da suke wa maƙiya aiki tare da fuskantar hukunci mai tsanani ga masu laifi (musamman masu alaƙa da abokan gaba) domin bisa doka anfani da irin waɗannan na'urori da doka ta hana laifi ne.

An kuma gano tare da kama sojojin haya 55 na gwamnatin Isra'ila a Hormozgan bayan sa idon leken asirin sojojin Imam Zaman (AS).

Sannan jami'an tsaron Iran sun kama mutane 7 a Borujen bayan ayyukan sumame da cibiyar leken asiri ta Chaharmahal da Bakhtiari ta gudanar inda ta an gano mutane 7 tare da kama su a matsayin manyan sojojin haya da suke yunkurin haifar da tarzoma a daren Larabae ƙarshen watan shekarar 1404 a birnin Borujen.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha