15 Maris 2026 - 00:14
Source: ABNA24
Irgc: Ta Harba Jiragen Yaƙi Marasa Matuƙa Don Gano Tare Da Kai Hari Kan Sojojin Amurka + Bidiyo

Ofishin Hulɗar Jama'a na IRGC: jiragen yaƙi marasa matuka tafi da gidanka masu bincike da kai hari kaitsaye na Rundunar Sojan Sama na IRGC suna ci gaba da gano wurin ɓoyewar sojojin 'yan ta'adda na Amurka a yankin.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A ayarin gungun makamai karo na 50 cikin yaƙin Wa'adis Sadiq4 wanda aka aiwatar da shi da ramzi mai albarka na (Ya Zahara'a Salamullahi Alaiha) tare da sadaukar da natijar wannan aiki ga manyan Shahidai Janar mai tsaron juyin juya hali shahidi Ali Shadmani da Maj. Gen. Haj Hossein Hamedani a kan sansanonin sojojin ta'addanci na Amurka da ke Al-Zufrah, da Fujairah, Jufair, da jirgin yaƙin ruwa na biyar, Ali al-Salim, Al-Azreq, da kuma kan na'urorin radars dake bayar da gargadin farko da ke a yankin da suka taka rawar kariya ga gwamnatin sahyoniyawa. An kai harin ne da jirage marasa matuka masu kai harin ƙunar baƙin wake na Rundunar Sojojin Juyin Juya Hali. 

Waɗannan Jiragen marasa matuka suna iya gano wuraren buya na sojojin ta'addancin Amurka a yankin, tare da daukar ingantattun bayanai. 

Ana bukatar mutanen yankin da su nisanci maboyar sojojin Amurka.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha