8 Maris 2026 - 16:42
Source: ABNA24
Hizbullah Na Ci Gaba Da Ruwan Makamai Akan Wuraren Isra'ila

Wasu kafofin watsa labarai na Isra'ila: a arewa; ruwan makamai masu linzami da ba su daina sauka na Hizbullah suna ci gaba da canja ma'aunan yin ƙaura a (yankin Arewa na Falasdinu da aka mamaye) Saboda tsamarin arangama tsakanin kungiyar Hizbullah da 'yan sahayoniya a garin Motula da ke kan iyaka, 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban majalisar birnin Mutula da ke arewacin Falasdinu ya ce: an shafe sa'o'i uku ana yaki kuma kungiyar Hizbullah ta yi ta kai hare-hare a duk fadin yankin. 

Hizbullah A mayar da martani ga keta iyakar Isra'ila, wacce ta kai hari ga birane da garuruwan Lebanon da dama da kuma yankunan kudancin Beirut, ta kai hari ga Barracks na Branit (Hedkwatar Rundunar 91st) tare da makami mai linzami a 01:45 na safe ranar Lahadi. 

A wani rahoton kuma Hizbullah cikin sauki suna ci gaba da aikewa da makamai masu linzami ba tare da wata matsalar katsewa daga gwamnatin Isra'ila 

Hizbullah ta kara da cewa Mayakan mu sun toshe hanyar ci gaban sojojin abokan gaba zuwa garin Eitun da ke kan iyaka ta hanyar harba bindigogi da makamai masu linzami. Kafar sadarwa ta Isra'ila 24 ta ce: Kungiyar Hizbullah ta harba makamai mai linzami masu yawa tun farkon yakin a jiya. Kungiyar Hizbullah ta yi arangama da gungun sahyoniyawa ƴan mamaya da ke kokarin shiga garin Eitron. Hezbullah ta ce mayakan gwagwarmaya sun sami damar kai hari kan sansanin sojojin Isra'ila da ke gaban garin da makami mai linzami, inda suka kashe tare da raunata wasu da dama daga cikinsu. 

A cikin Raneku da gwagwarmaya suka fi kai hare-hare akwai jiya asabar inda Hizbullah ta gudanar da ayyukan hare-hare 33 a kan maƙiyan sahyoniyawa sahyoniya ita ce ta farko da Hizbullah ta kai hari a kan sojojin abokan gaba a gabashin Lebanon wanda sojojin Isra'ila suka sha kayi a wannan arangama. 

A wani aiki daga Syria, mayakan sahyoniyawa sun yi niyyar tura dakaru a garin Nabi Seth da kuma nemo gawar matukin jirginsu da ya bace Ron Arad, wanda ya tsere daga yankin inda suka fuskanci martani daga Hizbullah a da mazauna yankin. 

Aikin Hizbullah na biyu, wanda ya gudana da karfe 3:45 na safiyar ranar Asabar, harin makami mai linzami ne a wata matattarar sojin abokan gaba a tsaunin Al-Muhams da yankin Khala Al-Asafir da ke kudu da Khayyam. 

An kunna na'urorin gargadi 17 a arewacin yankunan da aka mamaye bayan harin da jiragen sama marasa matuki da ƙungiyar Hizbullah ta kai.

Hizbullah Lebanon ta sanar da cewa ta harba makamai masu linzami 100 da jirage marasa matuka nau'in UAVs a yankunan da aka mamaye jiya. 

Sojojin Isra'ila sun kasa tare da gazawa wajen fuskantar jirage marasa matuka na Hizbullah inda sojojin suka fuskanci wahala wajen dakile jiragen da ba su da matuki da suka kai Tekun Haifa da Arewacin Acre. Daya daga cikin jirage marasa matuki ya afka wani gini kuma ya yi barna sosai ga Kibbutz Afron a Al-jalil 

A ƙarshen rahoton hare-haren makami mai linzami na kungiyar Hizbullah kan garuruwan Isra'ila sun bayar da rahoton cewa kungiyar Hizbullah ta kaddamar da hare-hare kan garuruwan da ke yankin Al-Jalil al-Ali. Bayan wadannan hare-haren, makamai masu linzami da dama sun afkawa garin Kafar Solad.

Your Comment

You are replying to: .
captcha