7 Maris 2026 - 23:53
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Harba Makamai Masu Linzami Sama Da 40 Kan Haifa Lokaci Ɗaya Da Kai Harin Iran

Gagarumar harba makamai da kungiyar Hizbullah ta yi ya baiwa 'yan sahayoniya mamaki inda kungiyar ta harba makamai sama da 40. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba makamai masu linzami fiye da 40 a Haifa a 'yan mintoci da suka gabata, wasu daga cikinsu masu nauyi ne. A sa'i daya kuma, Iran ta harba makamai masu linzami a yankunan da aka mamaye kuma an ji kararsu a duk fadin Isra'ila. 

Hizbullah Ta Harba Makamai Masu Linzami Sama Da 40 Kan Haifa Lokaci Ɗaya Da Kai Harin Iran

A gefe guda kuma Hizbullah ta fitar da sanarwar gargadi ga mazauna garuruwan Kariat Shamuna da Nahharia da ke arewacin yankunan da aka mamaye da su bar wadannan yankuna da wuri-wuri su tafi kudu tun kafin Hare-Hare su shafe su.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha