28 Faburairu 2026 - 18:01
Source: ABNA24
Iran: Ɗalibai 108 Sun Yi Shahada 92 Sun Jikkata 

An samu shahidai 85 da jikkatar mutane 92 a lokacin haɗa wannan rahoton a hare-haren Isra'ila da Amurka kan Iran

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gwamnan Minab: Biyo bayan hare-haren masu aikata laifukan ta'addanci na Amurka da na Sahayoniya a makarantar Shajreh Tayebeh da ke Minab, mutane 85 sun yi shahada a tashin farko, wasu 60 kuma suka jikkata. kuma ana ci gaba da cire tarkacen ginin da abin ya faru. 

Adadin tarkacen ginin yana da nauyi sosai. Babu kididdiga kan yawan malaman da suka yi shahada zuwa yanzu. 

Karin yawan shahidan makarantar firamare ta Shajreh Tayebeh da ke Minab, gwamnan birnin Minab ya ce: Yawan shahidan da Amurka da Isra'ila Sahayoniya suka kai wa makarantar firamaren 'yan mata na wannan birni na karuwa kuma ya kai ga shahidai 108 da jikkatar mutane 92 a lokacin haɗa wannan rahoton da karfe 5:00 na yamma; Akwai kuma wasu dalibai da dama a karkashin baraguzan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha