Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A wannan taron, Jakadan Iran ya gabatar da cikakken rahoto kan yadda zanga-zangar ta kasance tun daga ranar (28 ga Disamba).
Da yake magana kan fara zanga-zangar lumana ta 'yan kasuwa, ƙungiyoyi, da masu fafutukar tattalin arziki, da kuma martanin da gwamnati ta mayar nan take ta hanyar tattaunawa da matakan gyara, ya jaddada cewa bayan haka, 'yan ta'adda dauke da makamai da kuma wadanda aka tsarasu sun shigo wurin kuma suka jagoranci zanga-zangar zuwa ga tashin hankali da harbi kan jama'a da jami'an tsaro.
Bahreini ya kira waɗannan ayyukan ci gaba da salon "Yaƙin Kwanaki 12", wanda ke da nufin haifar da tsoma baki daga ƙasashen waje da kuma haifar da rashin tsaro a yankin Iran, ya ƙara da cewa: "Akwai shaidun sauti da takardu masu inganci na umarnin harbin fararen hula da waɗannan masu tarzoma su kai".
Da yake ambaton kalamai daga jami'an Amurka da Isra'ila, ciki har da Mike Pompeo da kafofin watsa labarai na Isra'ila a X-Net, wakilin Iran ya nuna hannun Amurka kai tsaye da gwamnatin Sahyoniya wajen tallafawa waɗannan ayyukan ta'addanci, yana mai kiran su da take hakki a sarari ga 'yancin kai da mutuncin yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Your Comment