Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An kai hari da lalata gine-ginen gwamnati 314. An kuma kona gine-ginen gwamnati 155. An lalata bankuna 399 kuma an kona bankuna 303.
An kai hare-hare sau 704 da lalata gine-ginen al'umma masu zaman kansu. Haka kuma, an kona gine-ginen mutane 384.
An wawushe manyan shaguna 419 a larduna 8, an lalata su, an kuma kona su.
An lalata tashoshin bas 253 wasu kuma an kona su.
An lalata gidajen mai 24 na masu zaman kansu wasu kuma an kona su.
An lalata babura 220 na talakawa wasu kuma an kona su.
An lalata motocin jigilar jama'a 305 kamar bas da motocin daukar marasa lafiya kuma an kona wasu 93.
An lalata motocin 'yan sanda 749 kuma an kona motoci 90.

An lalata masallatai 350 kuma an kona masallatai 134.
Dangane da wasu wuraren addini kamar Hussainiyoyi da Imamzadeh, an lalata wurare 36 kuma an kona wurare 48.
An kuma lalata ko kuma an kona makarantun hauza 89 a sassa daban-daban na ƙasar Iran wanda wannan ke nuna babban matsalar abokan gaba sune walwalar al'umma da kuma jagorancin addinin Musulunci da wuraren ibadar al'umma.
Your Comment