Imam musa As dan Imamu Ja’afar Assadik As wanda akewa lakabi da Alkazim ana masa ALkunya da Abul Hasan da Abu Ibrahim Shine Imam na Bakwai cikin Jerin A’immah da Manzon Rahama yabarmana, mahaifiyar an ace da ita Humaidah yar Saa’id mutuniyar Afrika.
Anhaifeshi a wani waje dake tsakain makka da madinah da Ake kira da Abwa’a a ranar 7/safar shekara ta 168h ya rayu shekaru 55 ya kuma dauki shekaru 35 yana mai rike da Mas’uliyyar Imamah
Imam ya rayu bisa kulawa da tarbiyyar mahaifinsa Imam Ja’afarussadik wanda tun yana karami alamomi na kwazo da hazaka da ilimi littafan tarihi sun kawo labarin wata tambaya da Abu Hanifah yayi masa alokacin da yana karami inda yace masa: Daga wa Sabo yake Gangarowa?
Sai yabashi amsa da cewa: Lalla babu makawa sabo yana ganganrowa ne daga Bawa ko ubangijinsa ko kuma daga garsu su biyun. Idan ta kasance daga ubangiji to shi mai adalci ne kuma yafi kowa yin adalci bazai zalunci bawansa da kama sa da abinda bai aikata shi ba, idan kuma daga garesu su biyun take to ta kaga yayi tarayya dashi akai to kaga wanda yafi karfi da daukaka shine yafi cancanta da yafiya ga rarrauna wato bawansa, idan kuma daga bawa ne sabon ya gangaro to kaga kansa lamarin yafada. Kuma kaga shi bawa anhanashi aikata sabo kaga shi ya cancanti abshi ladar aikin kirki da dana zunibi kuma akanshi shiga wuta da Aljanna yake tabbata.
Imam yafara gudanar da ragamar Imamancin sa bayan shahadar mahaifinsa Imam Jaafar As ashekarata 148h akarshen lokacin kalifancin Mansur Abbasy wanda yayi Imam yayi zamani da kalifofin da sukazo bayan Mansur wato Almahdi, Alhady, da harunar Rashid. Wanda alokacinsa aka shahadantar dahi bisa umarnin sa
Lokacin rayuwar Imam As ya dace da lokacin da daular Abbbasawa takeda karfinta na Zalunci da muzgunawa AL’umma wanda Imam yadauki matakin yin takiyya a ayyukokinsa kuma ya umarci mabiyansa da yin hakan saboda su kasance cikin aminci inda bai yadda ya yakasnce cikin masu yin zangazanga na yan shia data rinka faruwa alokacinsa inda yayi kokarin assasa wakilai a garuruwa da dama domi su wakilceshi da kuma samun saukin sadarwa atsakanin su, har wala yau kuma lokacinsa ya dace da bayyanar kungiyoyi da dama na shia kamar ismailiyya, fadahiyya, nawusiyya bayan shahadarsa kuma kungiyar wakifiyyah ta bayyanah.
Anyi wa Imam lakabi da Kazim ne saboda hadiye fushin da yake dashi inda littafn tarihi suka shaida da yawan Iliminsa da ibadarsa da kyautarsa da hakurinsa.
Inda aka kama imam sau biyu bayan tuhime tuhume da makiyansa suka kai wajen khalifa haruna inda yasanshi cikin kurkun Isah danJa’afar dake basara bayan antaho dashi daga madina bayan wani lokaci kuma aka maidashi kurkukun fadl dan rabii dake bagdag sannan aka maidashi na fadli dan yahaya sannan kurkukun Sinde dan SHahik wanda acikinsa yayi shahada salamullahi Alaihi dake
Imam yayai shahada a ranar 25 ga watan rajab a Birnin Bagdaz shekara ta 183h kabarin Imam yana yankin Kazimiyyah dake Iraki wanda a wannan ranar da ake tunawa da shahadar an kaiwa masu zuwa ziyararsa hari wato talata 25g/ rajab shekara ta 1442h.
Juyayin Wafatin Sayyid Abu Dalib (as) 26/ Rajab Shekara 10 Bayan Aiko Annabi (Sawa)
A irin wannan Rana ne dai 26 ga watan rajab shekaru goma bayan aiko Annabi (sawa) Sayyid Abu Dalib Mu’umini Ali Muhammad (sawa) yayi wafati.
Sunan sa Abdulmunaf dan Abdul Mudallib dan Hashim Mahaifi ga Imam Ali As kuma Baffa ga Annabin Rahama S wanda yabashi kariya da kulawa tundaga wafatin Babansa har zuwa lokacin da yayi wafati yak are shi daga dukka cutarwa ta Mushirikan labarawan Kuraishawa. Matarsa ita ce Fatimatu bint Asad Mahaifiyar dukan yayansa guda tara mata 5 4 maza.
An Haifeshi A Shekaru 88 Kafin Hijirar Manzon Allah Sawa Shekaru 35 Kafin Haihuwar Annabin (Sawa).
Ya kasance madaukaki a cikin shugabannin mutanan Makka da Kuraishawa da ma bani Hashim gaba daya. Hamshakin dan kasuwa, ya rike matsayin Shayarwa da Masaukin Dukkan mahajjata Kafin Aiko Annabi Sawa malaman tarihi sun kawo cewa ya kasance Shugaba ne da ake masa biyayya mai Kwarjini ne shi ga kuma yawan Kyauta da Ciwarwa hatta ya kasance duk ranar da yake ciyarwa a Makka babu mai ciyarwa. Kamar yadda ya ke sannan ya kasance da danginsa suna kan Addinin Annabi Ibrahim As ba su kauce a kansa ba shine wanda ya sunnata bayar da diyya ga iyalan wanda aka kashe kuma musulunciya tabbatar da wanann hukunci nasa, ya haramtawa kansa shan giya kamar yadda yazo Sirah Halbiyyah. Kamar yadda kulawarsa ga Annabin rahama (saw) da gudunmawar da bayawa Addinin Allah a bayyane ya ke bayaninsa na cikin littafan tarihi.
Yayi wafati kwana 3 da wafatin Sayyidah Khadija As lokacin da yai wafati yana dan shekara 85 bayan zuwan labarin wafatinsa ga manzon Allah (sawa) yayi bakin ciki sosai in da Annabi yake cewa: Kuraishawa masu iya cimmani ba sai da Abu dalib yayi wafati, bayan nan sai ga sakon Ubangiji tare da Jabrail As yana mai bawa Annbai (sawa) umarni akan ya fita daga Makka saboda mai taimaka maka yayi wafati kamar yadda wanan shekarar Annabi (sawa) ya kirata da Shekarar Bakinciki an kuma binne shi a Makabartar Hujun.
Your Comment