Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin sakonsa, Raji ya jaddada cewa "zaman lafiya da wadata su ne abin da Lebanon, Iran, da dukkan yankin ke bukata," yana mai kira da a samar da "sabon babi a dangantaka tsakanin kasashen biyu".
Ministan Lebanon ya bayyana "sha'awarsa ta kafa tattaunawa ta gaskiya wacce ke karfafa aminci tsakanin Lebanon da Iran (...) da kuma bukatar dangantakar ta dogara ne akan wata hanya mai ginuwa bisa girmama juna tsakanin kasashen biyu".
Ya kara da cewa "ya kamata a gudanar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin biyu da kuma cibiyoyinsu na hukuma, ta hanyar da za ta kiyaye 'yancin kai da 'yancin kowanne daga cikinsu da kuma cimma walwalar al'ummar Lebanon da Iran".
Your Comment