24 Disamba 2025 - 21:25
Source: ABNA24
Turkiyya Na Shirin Tunkarar Isra'ila

Tsohon jami'in diflomasiyyar Isra'ila: Sakonnin Isra'ila sun ƙara zafafa barazana ga Ankara kuma sun haifar da haɓaka da bunkasa tsarin tsaron sararin samaniyar Turkiyya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Alon Leal, tsohon jami'in diflomasiyyar Isra'ila, a cikin wata sanarwa: Turkiyya na haɓaka tsaron sararin samaniyarta da sojojin sama don mayar da martani ga gargaɗin Isra'ila kuma ƙasar tana shirin fuskantar rikici da Isra'ila.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Larabawa, ya yi ishara da cewa saƙonnin Isra'ila sun ƙara karfafa barazanar a Ankara kuma sun haifar da haɓaka tsarin tsaron sararin samaniyar Turkiyya.

Leal ya kuma nuna damuwa game da haɗarin rikicin soja a Siriya da rawar da Turkiyya ke takawa a Gaza, kuma ya jaddada cewa ƙarfafa haɗin gwiwar sojojin Turkiyya da Azerbaijan na iya haifar da ƙaruwar tashin hankali.

Your Comment

You are replying to: .
captcha