11 Disamba 2025 - 14:37
Source: ABNA24
Yaƙin Basasa Na Iya Ɓarkewa A Siriya A Kowane Lokaci.

Wani mai fafutukar siyasa a Siriya ya yi gargaɗin cewa ɗaukar fansa da 'yan ta'addar Takfiriyya suke yi yana ƙara haɗarin yiwuwar yaƙin ƙabilanci a Siriya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar rahotannin kafofin watsa labarai, mai fafutukar siyasa a Siriya Tariq al-Ahmad ya yi gargaɗi game da ƙaruwar rikice-rikicen addini da rarrabuwar kawuna a cikin ƙasar. Ahmad ya bayyana cewa Siriya na cikin wani yanayi mai haɗari, inda rikicin ƙabilanci da rikicin mai tsanani za su iya ɓarkewa a kowane lokaci.

Ya ƙara da cewa rarrabuwar kawuna da rikice-rikicen cikin gida sun ƙaru sosai sakamakon ayyukan ɓangarorin da al-Julani ke jagoranta.

Ya nuna cewa ana yanke kudiri ne a ƙasar ne daga mahangar soja, ba bisa ga nufin mutane ba. Ɗaure tsoffin jami'an shari'a misali ne bayyananne na take haƙƙin ɗan adam.

Al-Ahmad ya jaddada cewa ana kai hari ga tsirarun 'yan a ƙasar, ana tsananta musu, kuma ana fuskantar tashin hankali. Mutanen Siriya suna burin samun Siriya mai zaman kanta, mai dimokuraɗiyya wacce ba ta da bambancin ra'ayi. Ya kammala da cewa mataki na gaba zai haifar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ko kuma ya ƙara ta'azzara rikicin ƙabilanci a ƙasar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha