Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: An gudanar da zanga-zanga a biranen Morocco wanda da dama na al'ummar kasar sun fito domin yin Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaiwa yankin Zirin Gaza, kuma kasashen yankin da dama sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga gwagwarmayar Palasdinawa.
Biranen da suka hada da Tangier, Casablanca, Tetouan, Marrakesh, Kenitra, Fez, Meknes, da Agadir suma sun shaida zanga-zangar da aka gudanar da mafi yawansu bayan sallar Juma'a. Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da yadda fararen hula ke ci gaba da fama da yunwa a zirin Gaza da kuma rufe mashigar kan iyaka.
A gaban majalisar dokokin Morocco da ke Rabat babban birnin kasar, mahalarta taron sun rera taken yin Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa kasashen Larabawa tare da neman a hukunta shugabannin mamaya kan laifukan da suka aikata.
Masu zanga-zangar sun daga tutocin Falasdinawa da hotunan shugabannin gwagwarmaya, inda suka bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu tare da yabawa kungiyar ta Global Steadfastness Flotilla da ta tashi zuwa Gaza da mahalartanta.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da su soke yarjejeniyoyin daidaitawa da aka kulla da Isra’ila, tare da yin kira ga al'ummar Larabawa da na Musulunci da su kaurace wa kayayyakin mamaya da kamfanonin da ke tallafa mata.
A Nouakchott babban birnin kasar, daruruwan 'yan kasar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza da kuma yin tir da kisan kare dangi da Isra'ila ke yi.
An gudanar da zanga-zangar bayan sallar Juma'a a gaban babban masallacin birnin Nouakchott, inda mahalarta taron suka yi ta rera taken kin amincewa da shirun da shugabannin kasashen duniya suka yi kan kisan kiyashin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza.
Taken da aka rera sun hada da "Daga Chinguetti, gaisuwa...ga Gaza mai alfahari," "kakaba yunwa a Gaza laifi ne na yaki," da taken a "Dakatar da yaki."
Masu zanga-zangar dai sun dora alhakin kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ga Amurka, tare da jaddada bukatarsu na korar jakadan Amurka daga birnin Nouakchott.
An kuma gudanar da jerin gwano a titunan birnin Tripoli na arewacin kasar Labanon mai taken "Ba za mu bar Gaza ita kadai ba," a matsayin martani ga kiran kwamitin tallafawa Al-Aqsa mai zaman kansa.
Tattakin ya taso ne daga dandalin Abdul Hamid Karami da ke tsakiyar birnin ya nufi kan titunan da ke makwabtaka da shi.
Sheikh Nasser al-Tikriti yayi bayani a gefen tattakin da cewa: "Muna sake tattakawa domin shaida wa mutanenmu a Gaza cewa ba ku kadai ba ne".
Al-Tikriti ya kara da cewa, "Muna cewa, kada ku yanke kauna, ku yi hakuri, ku daure, kuna karantar da dukkanin duniya ma'anar tsayin daka ta fuskar gaskiya".
Dubban daruruwan al'ummar kasar Yemen ne suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Sana'a da wasu larduna da dama, inda suka yi tir da yin shuru da kasashen duniya da na Larabawa suka yi dangane da kisan kiyashin da ake yi a Gaza.
Ana shirya zanga-zangar ne duk sati domin amsa kiran da shugaban kungiyar Ansarullah (Houthis) Abdulmalik al-Houthi ya yi mai taken "Tare da Gaza ba za mu amince da abin kunyar cin amana ba, ko da kuwa laifuffukan wuce gona da iri sun kai inda suka kai".
Masu zanga-zangar sun daga tutocin Yemen da na Falasdinu tare da daga tutocin da ke nuni da yin Allah wadai da shirun da jagogorin kasashen duniya suke yi dangane da wuce gona da iri da Isra'ila ke yi da kisan gilla da tilasta kaurawa al'ummar Palasdinu.
A cikin wata sanarwa da suka gabatar a wajen zanga-zangar Sana'a, masu zanga-zangar sun tabbatar da ci gaba da zanga-zangar da suke yi duk mako na nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ake zalunta...da kuma nuna adawa da makiya sahyoniyawa masu muggan laifuka.
Sanarwar ta kuma yaba da irin tsayin dakan da al'ummar Palastinu suka yi kan wuce gona da irin na Isra'ila tare da sanya albarka da yabo ga ayyukan soji da dakarun Ansarullah suka kai wa Isra'ila.
Tare da goyon bayan Amurka, Isra'ila ta fara aiwatar da kisan kiyashi a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 65,174 tare da raunata 166,071, yawancinsu yara da mata, da kuma dubban daruruwan dubbai.
Your Comment