19 Satumba 2025 - 16:22
Source: Quds
Shahidi 1 Masu Rauni 3 A Harin Isra'ila Ga Labanon 

Mutum daya ya yi shahada, uku kuma suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai kan kasar Labanon

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran kasar Labanon sun rawaito a yau Juma'a cewa wani dan kasar Lebanon ya yi shahada tare da jikkata wasu uku a wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a kudancin kasar Lebanon.

Harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan wata mota a gaban asibitin gwamnati na "Tibneen" da ke kudancin kasar Lebanon.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mutum daya ya yi shahada yayin da wasu uku suka jikkata a harin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha