19 Satumba 2025 - 19:40
Source: ABNA24
MDD: Ta Dawo Da Aiwatar Da Takunkumai A Kan Iran

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Zai dawo da kudurinsa akan Iran a ranar Asabar 27 ga Satumba, 2025 da karfe 04:30 na safe agogon Tehran.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da wani kudiri na neman dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran din.

Sakamakon zaben kaɗa kuri'ar a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zo kamar haka:

Kuri'u 4 da suka amince da dagewa Iran takunkuman sune kamar haka: China, Rasha, Pakistan, da Aljeriya

Kuri'u 9 da suka ki amincewa: Birtaniya, Faransa, Amurka, Saliyo, Slovenia, Denmark, Girka, Panama, da Somalia

Kuri'u 2 sun kin yin zaɓen sune kamar haka: Guyana da Koriya ta Kudu

Dangane da hakan ƙasar Rasha ta ce: Ba mu amince da mayar da takunkumin da aka kakaba wa Iran ba

Wanda Wakilin na Rasha ya tabbatar da haka da cewa: rashin amincewa da kudurin game da ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran din da cewa ba shi da wani tushe a dokan ce. sannan ya ce Rasha ba ta amince da mayar da takunkumin ba.

Shima Wakilin kasar Sin a komitin sulhu ya ce: Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar, ta kai wa Iran hari ta hanyar soji, ta kuma kawo cikas ga tattaunawar.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dai ya yanke shawarar sake kakabawa Iran takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla a 2015.

Wadannan takunkumin za su fara aiki ne a ranar 27 ga Satumba da karfe 8 na dare agogon New York.

Ya kamata a lura da cewa Zarif ya musanta cewa akwai wata hanyar da za ta iya sanyawa a dawo da takunkuman na JCPOA, kuma shima tsohon shugaban Hassan Rouhani ya ce an dage takunkumin kuma ba zasu taba dawo ba!

Javad Zarif, a ranar 19 ga Satumba, 2020, ya musanta samuwar takunkuman a cikin JCPOA inda ya ce:

Ba wani batun takunkumai ko wani makamnacinsa a cikin JCPOA da tattaunawar kawai farfagandar Amurka ce. Sun ce za mu yi sanarwar dai, kuma bayan wata guda za a dawo da kudurori, amma ba haka lamarin yake ba!

Hassan Rouhani ya kuma ce a yakin neman zabensa na wa'adi na biyu a watan Mayun 2021, yana mai jaddada dage takunkumin: Takunkumin ba zasu dawo ba.

A halin yanzu, takunkumin da ya fi takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Iran daga kasashen Turai da Amurka, kuma ta fuskar tattalin arziki, mayar da takunkuman na Majalisar Dinkin Duniya ba zai yi wani tasiri fiye da da ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha