30 Yuli 2025 - 22:56
Source: ABNA24
IRGC: Zamu Mayar Da Martani Mai Gauni Tare Da Canja Fagen Yaƙin

Kakakin IRGC: Martanin Iran idan aka sake kai harin ta'addanci zai zama mafi muni kuma zai canza wajen yaƙin.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Kakakin IRGC, a martani da yayi ga barazanar Isra'ila na baya-bayan nan ya ce:

Idan har gwamnatin yahudawan sahyoniya ta sake kai hari kan tsaron kasar Iran, ba wai kawai za ta samu martani mai tsauri ba ne, a'a sai dai yanayin martani da fagen fama na iya canzawa.

A yakin na kwanaki 12, numfashin gwamnatin Isra'ila yana gab da karewa, kuma idan suka maimaita kuskuren da suka yi, ba za su sami damar barin matsugunansu ba. Dabarar da aka yi a ƙarshen yaƙin tana hannunmu, kuma ba za'a ƙararrawa a yankunan mamaye ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha