Jagora: Addini Da Ilimi Da Hadin Kan Al'ummar Iran Ke Da Shi Silar Kiyayyar Makiya
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: a daidai lokacin da ake cika kwanaki 40 na shahidan yakin kwana 12 da gwamnatin Amurka Da Isra’ila suka kakabawa al'ummar Iran, a yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gudanar da taron tunawa da wadannan shahidai a Husainiyar Imam Khumaini (RA) bisa halartar iyalan shahidai da kuma wasu bangarori na jama'a da jami'ai daban-daban.
A jawabin da ya yi a wajen taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan yaki a matsayin wani abu da ya bayyana iko da karfin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi da kuma nuni da irin karfi na kafuwar tushen ta da ba ya misaltuwa. Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa babban abin da ke haifar da kiyayyar makiya shi ne adawar da masu mugun nufi suke da shi ga imani da ilimi da hadin kan al'ummar Iran ne, ya ce: Da taimakon Allah al'ummarmu ba za su yi watsi da tafarkin karfafa imani da fadada ilimi daban-daban ba, kuma tare da bakincikin makiya za mu iya kaiwa ga kololuwar ci gaba da daukaka.
Yayin da yake bayyana sabon ta'aziyya ga iyalan da su kai saura na wadanda su kai shahada na kwamandojin soji, da masana kimiyya, da ababen kauna a yakin baya-bayan nan, Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kasar Iran Baya ga irin gagarumin daukaka da ta samu a cikin wadannan kwanaki 12, wadanda duniya baki daya ta tabbatar da su a yau, al'ummar Iran sun sami damar nuna wa duniya irin karfin da suke da shi, da juriyarsu, da azamarsu, da kuma irin karfin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu na baya-bayan nan.
Haka nan kuma ya dauki tsayin daka da dakewa juriya na musamman na tushen tsarin Jamhuriyar Musulunci a matsayin wata fa'ida ta yakin baya-bayan nan, inda ya kara da cewa: Wadannan al'amura ba su taba faruwa a gare mu ba a cikin shekaru 46 da suka gabata, baya ga yakin shekaru 8 da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha fuskantar abubuwa da suka hada da juyin mulki, da tayar da tarzoma daban-daban na soji, da siyasa da na tsaro, da tilasta raunanan makiya su dauki mataki a kan al'umma, tare da tarwatsa shirin dukkanin makiya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira kafuwar tushen tsarin Musulunci a kan tushe guda biyu na "addini" da "ilimi" yana mai cewa: Al'umma da matasan Iran bisa dogaro da wadannan tushe guda biyu sun tilasta makiya ja da baya a fagage daban-daban, kuma za su ci gaba da yin hakan daga yanzu zuwa na gaba ma.
Ya yi la'akari da babban dalilin adawar da masu girman kan duniya suke, a sahun gaba Amurka masu aikata laifuka, ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne addini da ilimi da hadin kan Iran a karkashin inuwar kur'ani da Musulunci, ya ce: Abin da suke gabatar da shi a matsayin makaman nukiliya da wadatuwar sinadari da batun hakkin dan Adam wani fakewa ne da guzma.
Yayin da yake jaddada cewa al'ummar Iran ba za su yi watsi da addininsu da iliminsu ba, tare da taimakon Allah, Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Za mu dauki matakai masu girma wajen karfafa addininmu da fadadawa da zurfafa ilmummuka daban-daban, sannan za mu iya kai Iran ga kololuwar ci gaba da daukaka bisa turmusa hancin makiya.
A wajen wannan toron, da dama daga cikin masu karatun kur’ani sun karanta ayoyin kur’ani mai tsarki, sannan Hujjatulleslam Rafi’i bisa dogaro da Huduba ta 182 ta Nahjul-Balagha, ya yi ishara da sifofin shahidan yakin Siffin a cikin jawabinsa, ya kuma dabbaka wadannan siffofi da suka yi daidai da shahidan yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan.
Tsayuwa akan tafarki, tafiya akan tafarkin gaskiya, karatun alqur'ani da aiki da shi, da ayyukan farilla, raya sunnoni na Ubangiji, fuskantar bidi'a, shiga jihadi, da bin jagoranci sun kasance siffofi guda takwas wadanda Hujjatuleslam Rafi'i ya ambace su da cewa: A cewar Alkur'ani, imani da tawakkali su ne muhimman abubuwa guda biyu na samun nasarar Allah kuma wadannan abubuwa biyu sun bayyana a yakin kwana 12, kuma su suka share fagen tsayin daka da nasarar al'ummar Iran.
A wajen wannan taro, Malam Muhammad Reza Bazri ya karanta kasidu na jinjinaga shahidan yakin da makiya yahudawan sahyoniya suka aikata tare da nuna alhini kan irin musibun da al'ummar Allah suke sha.
Your Comment