Ka-ce na-ce da Iran ka iya samarwa Azarbaijan wacce ke bin sahun Isra'ila da Amurka asara mai tsadar gaske,. Mujallar Foreign Affairs ta Amurka ta bayar da rahoton cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasashe kalilan a duniya sun ga matsayinsu a yankin ya canza sosai kamar kasar Azerbaijan, amma nasarorin da ta samu a duniya bai kubutar da ita daga raunin cikin gidan da take ciki ba.
Mujallar Foreign Affairs ta Amurka ta yi nuni da irin hadarin da ke tattare da gwamnatin Aliyev, inda ta rubuta cewa, Isra'ila, da kusancin diplomasiyya da Amurka, da kuma iyakarta da Iran, ya sa Baku ta yi imani da cewa..." Azabaijan babbar abokiyar hulda ce ga Amurka, musamman ganin yadda gwamnatin Aliyev ta goyi bayan nasarar da Trump ya samu a zaben, tana mai imani cewa zai dauki mataki mai tsauri waje kishiyantar Iran.
Rahoton ya kara da cewa "wannan sabani na iya zama mai tsada ga Azarbaijan, idan har takun saka tsakanin Iran, Isra'ila da Amurka suka kara ta'azzara, Tehran na iya mayar da martani ga matakin gwamnatin Aliyev da daukar mataki kai tsaye ko kuma tada tarzoma a cikin kasar Azarbaijan".
Your Comment