Falasdinu: A Gaza, Tsananin Ciwo Ne Da Zafi Da Hawaye Da Yunwa Kawai".

Mutane Miliyan 2.3 A Gaza Ba Tare Da Abinci Ba
22 Yuli 2025 - 19:19
Source: ABNA24
Falasdinu: A Gaza, Tsananin Ciwo Ne Da Zafi Da Hawaye Da Yunwa Kawai".

Kakakin Hukumar Kare Fararen Hula: Mun Sha Gargadin Duniya Da Su Dauki Matakin Dakile Yunwa Da Ke Ci Gaba Da Kashe Mu, Muna Gaya Muku A Fili Cewa A Zahiri Yaran Gaza Na Mutuwa Saboda Yunwa.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa, kakakin hukumar tsaron farar hula ta Gaza ya sanar a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Aljazeera cewa, mutane miliyan 2 da dubu 300 a Gaza ba su da biredin da zasu ci kuma suna fama da matsananciyar yunwa. Ya ce: "A Gaza, tsananin ciwo ne da zafi da hawaye da yunwa kawai".

Kamar yadda shafin sadarwa na Aljazeera ya kawo cewa, mun sha gargadin duniya da su dauki matakin dakile yunwa da ke ci gaba da kashe mu, muna gaya muku a fili cewa a zahiri yaran Gaza na mutuwa saboda yunwa.

Kakakin hukumar tsaron farar hula ta Gaza ya jaddada cewa dukkan mazauna Gaza miliyan 2.3 ba za su iya samun ko da biredin da zasu ci ba. Ana ci gaba da wannan mummunan yanayi yayin da Isra'ila ke haifarwa na ci gaba da killace yankin sannan kuma an dakatar gudanar ayyukan jin kai ga Gaza.

Ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa don dakile wannan bala'in jin kai da kuma kawo karshen killace Gaza.

Kakakin hukumar tsaron farar hula ta Gaza ya jaddada cewa ci gaba da wannan lamari na iya haifar da bala'in rasa rayuka.

Gaza dai ta shafe watanni tana fuskantar matsanancin halin halin rayuwa mai ban tausai, kuma al'ummar yankin musamman kananan yara na rayuwa cikin mawuyacin hali. Mummunan karancin abinci da ruwa da magunguna sun jefa rayuwar mutane da dama cikin hadari.

Kungiyar kare fararen hula ta Gaza ta sake jaddada bukatar kawo karshen killace Gaza da kuma tabbatar da samun damar kai kayan agaji, tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa na ceto rayukan al'ummar Gaza da ba su ji ba ba su gani ba.

Rahotanni sun ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na kai hare-hare kan cibiyoyin rarraba kayan agaji da kuma wuraren zama tare da hana kaiwa da isar kayan agajin jin kai Gaza. Wadannan hare-haren dai sun kara ta'azzara matsalar rashin kayan jin kai a Gaza.

Hukumomin cikin gida da na kasa da kasa da kuma kwamitocin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga kasashen duniya da su matsa tare d farkawa da yunkurawa wajen matsa lamba ga gwamnatin sahyoniyawa na dakatar da yakin kisan kare dangin da takeyi a Gaza bisa goyon bayan kasashen rturai Musamman Amurka da Ingila.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha