Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: sakon da ofishin hulda da jama’a na dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran (IRGC) ya fitar biyo bayan zango na goma na martanin Alkawarin Gaskiya 3 ya zo kamar haka.
بسم الله الرحمن الرحیم
فَمَنِ اعْتَدَیٰ عَلَیْکُمْ فَاعْتَدُوا عَلَیْهِ بِمِثْلِ مَا اعْتَدَیٰ عَلَیْکُم
سوره بقره (آیه ۱۹۴)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
Don haka duk wanda ya keta muku hurumi, to ku keta masa nasa hurumin kamar yadda ya yi muku
Suratul Baqarah (aya ta 194).
A martani ga harin sojojin yahudawan sahyoniya suka kai kan hurumin kasar musulunci ta Iran, mayakan sojojin sama na IRGC sun kai hari kan sansanonin sojin sama wadanda akai anfani da su wajen aiwatar da wannan hare-haren a karo na goma na alkaarin gaskiya 3 ta hanyar tsarawa da aiwatar da aiki mai tasiri.
Har ila yau, ta ba da sanarwar cewa za a ci gaba da waɗannan hare-haren anan gaba, mai sarƙaƙƙiya, mai nau'i-nau'i kuma sannu a hankali.
Kuma tabbas nasara tana daga Allah, Mabuwayi, Mai hikima
وَمَا النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِندِ اللَّهِ الْعَزِیزِ الْحَکِیمِ
Hulda da jama'a na dakarun kare juyin juya halin Musulunci
Your Comment