19 Yuni 2025 - 14:34
Source: ABNA24
An Gano Wata Mota Dauke Da Ƙananan Jiragen Ƙunar Baƙin Wake A Tehran

Mai magana da yawun yan sanda a Tahran ya sanar da gano mota ɗaukar kaya mai girma cike da ƙananu jiragen kai hari masu yawa. 

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Sardar Saeed Sa'id dangane da wannan aikin yace: "Abokan aikinmu sun gano tare da cafke wannan mota mai ɗauke da ƙananun jiragen kai harin da makiya suke anfani da su a wani aiki a yammacin Tehran. Sun kuma kama ma'aikacin Mossad. 

Ya ce: mutane za su iya sanar da duk wani shige da fice na mutanen da suke shakku akansu ga cibiyar 'yan sanda ta hanyar kiran wannan numbar 110.

Your Comment

You are replying to: .
captcha