Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, ganawar da jam'iyyun Haredi suka yi da wakilin gwamnatin Netanyahu da kuma mai ba da shawara kan harkokin shari'a na Knesset ya kare ne ba tare da an cimma matsaya kan dokar soja ba, kuma wakilan Haredi sun bar taron cikin bacin rai.
Jaridar Jerusalem Post ta bayar da rahoton cewa, shugabannin jam'iyyun adawa na Knesset a Isra'ila na shirin kada kuri'a kan kudirin a yau a majalisar Knesset, inda suka yi watsi da bukatar Netanyahu na dage kada kuri'ar rushe Knesset na tsawon mako guda.
Aryeh Deri, shugaban jam'iyyar Haredi Shas, ya gana da Benjamin Netanyahu a 'yan mintoci kadan da suka gabata, domin cimma matsaya kan abubuwan da doka ta kunsa na kebe Haredis daga aikin soja da kuma hana rusa majalisar dokokin kasar.
Wakilan jam'iyyar Shas kuma suna tattaunawa da bangaren Agudat Yisrael na jam'iyyar United Torah Judaism domin hana kada kuri'a kan kudirin. A gefe guda kuma Manyan ministocin gwamnatin Isra'ila sun yi kira ga Netanyahu da ya kawo karshen yakin Gaza
Tashar talabijin ta Channel 12 ta gwamnatin Isra'ila ta sanar da cewa wasu manyan ministocin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi kira ga Netanyahu da ya fara kawo karshen yakin da ake yi da zirin Gaza.
Your Comment