10 Yuni 2025 - 23:23
Source: ABNA24
Iran Da UNICEF Sun Rattaba Hannu Kan Inganta Yanayin Yara Da Matan Afghanistan A Iran

UNICEF da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iran sun dauki wani muhimmin mataki na inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya da tallafawa yara da mata 'yan gudun hijirar Afganistan a Iran tare da rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbayt (As) - ABNA - ya habarta cewa: ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da nufin tallafawa 'yan gudun hijirar Afganistan da ke Iran.

Shugaban cibiyar kula da harkokin jama'a ta ma'aikatar harkokin cikin gida Nader Yarahmadi da kuma Monica Oldan, wakiliyar UNICEF a Iran ne suka sanya hannu kan wannan takardar hadin gwiwa a jiya.

Bisa wannan takardar, bangarorin biyu sun himmatu wajen aiwatar da shirye-shirye a fannonin ilimi, kiwon lafiya, da tallafin zamantakewa ga kananan yara da mata na Afganistan.

A yayin taron, Yarahmadi ya jaddada cewa, ba a aiwatar da wannan hadin gwiwa ta fuskar kudi ba, sai dai don yin amfani da kwarewar UNICEF wajen samar da ayyukan yi ga 'yan gudun hijira.

Sabanin haka, wakiliyar UNICEF ta bayyana cewa, Iran ta dade tana karbar bakuncin daya daga cikin mafiya yawan 'yan gudun hijira a duniya, tana mai jaddada bukatar bayar da cikakken tallafi ga dukkan yara, ba tare da la'akari da kasarsu ba.

Wannan takardar za ta share fagen aiwatar da shirye-shiryen tallafi a duk fadin kasar Iran, da suka hada da samar da ilimi, inganta harkokin kiwon lafiya, da kuma shirye-shiryen tunkarar duk wata tabarbarewa.

Bisa kididdigar da aka yi a hukumance, a halin yanzu Iran na karbar bakuncin 'yan kasar Afghanistan fiye da miliyan 6, wadanda miliyan 2.1 ne kawai ke da izinin zama a dokance.

Your Comment

You are replying to: .
captcha