Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya nakalto daga Kamfanin dillancin labaran IRNA daga shafin sadarwa na Aljazeera Qatar cewa, kafofin yada labaran kasar Isra’ila sun bayyana cewa: dubban masu zanga-zangar ne suka taru a birnin Tel Aviv, inda suka bukaci a dawo da fursunonin Isra’ila, da kawo karshen yakin Gaza da kuma kawar da Netanyahu.
Zanga-zangar na zuwa ne kwana guda bayan yunkurin da yaci tura na jam'iyyun adawa na rusa majalisar Knesset ta Isra'ila. Rushewar da ka iya kawo karshen majalisar ministocin Isra'ila a halin yanzu, ba ta samu kuri'a ba saboda adawar mambobin majalisar Knesset 61 (majalisar dokokin Isra'ila).
Tashar talabijin ta 14 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, masu adawa da majalisar ministocin kasar sun gaza zartar da kudirin rusa majalisar dokokin Isra'ila (Knesset), inda 'yan majalisa 61 suka kada kuri'ar kin amincewa da kudirin.
Kafin kada kuri'a, jam'iyyun Haredi sun sanar da cewa za su yi adawa da kudirin bayan Yuli Edelstein, shugabar kwamitin kula da harkokin waje da tsaro na Knesset, ta sanar da cewa an cimma yarjejeniyoyin farko kan dokar aikin soja ta tilas.
Jam'iyyun adawa a majalisar ministocin Isra'ila da suka hada da Yesh Atid da Yair Lapid ke jagoranta da kuma Yisrael Beitenu (gidanmu na Isra'ila) karkashin jagorancin tsohon ministan tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman, sun bayyana aniyarsu a ranar Larabar da ta gabata na gabatar da kudirin rusa majalisar dokokin kasar.
A ranar 4 ga watan Yuni, jam'iyyar adawa ta Yesh Atid ta gabatar da bukatar gudanar da kuri'a kan rusa majalisar Knesset a ranar 11 ga watan Yuni.Yair Golan, shugaban jam'iyyar "Isra'ila Democrats", ya kuma bayyana cewa yakin Gaza ya kasa cimma manufofinsa, kuma ya zama yakin siyasa da nufin kiyaye majalisar ministocin "Benjamin Netanyahu", wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo. Jam'iyyun adawa a majalisar ministocin gwamnatin sahyoniyawan a halin yanzu sun zargi firaminista Netanyahu da neman a samar da wata doka da ta kebe Haredis daga aikin soja domin amsa bukatun jam'iyyun "Shas" da "United Torah Judaism" wadanda mambobi ne na kawancen da ke mulki, domin hana rugujewar majalisar ministocinsa ta hanyar kiyaye kwanciyar hankali.
Your Comment