19 Mayu 2025 - 14:39
Source: ABNA24
Pakistan: Harin Bam Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 24

Wani harin bam da aka kai a yankin Balochistan na Pakistan ya kashe mutane 24

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sandan Pakistan Abdullah Riaz ya ce wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wata kasuwa da ke Balochistan a kudu maso yammacin kasar, inda mutane hudu suka mutu tare da jikkata 20. Shagunan da ke kusa da kasuwar kuma sun lalace.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa, mai yiyuwa ne dakarun 'yantar da yankin Balochistan (BLA) suka kai harin. Idan dai ba a manta ba, ana kai hare-hare da makamai a Pakistan, musamman a lardunan Khyber Pakhtunkhwa da Balochistan, wadanda ke kan iyaka da Afghanistan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha