ABNA24 : Kakakin gwmanatin kasar ta Mali Haruna Mamadu Touri ya ci gaba da cewa; Da akwai dokar ta baci a kasar ta fuskar kiwon lafiya wacce za ta ci gaba da aiki na tsawon watanni shida.
Har ila yau Turi ya ce; Za a sake rufe dukkanin makarantun kasar har zuwa 10 ga watan Janairu na sabuwar shekarar da za a shiga.
Wasu wuraren da sabon kullen zai shafa sun hada da gidajen cin abinci, gidajen shan barasa da wuraren casu. Haka nan kuma an hana tara mutanen da su ka haura 50 a duk wasu taruka da suka hada daurin aure, jana’iza da makamantansu.
342/