ABNA24 : Kafafen yada labarai na ciki da wajen kasar sun nakalto bayanai daga hukumar wacce take nuna cewa tana shirin sallamar duk wani dansanda da yaki komawa bakin aiki shi. Hukumar tace wannan labarin ba gaskiya bane.
An kashe jami’an ‘yansanda 22 a tarzoman da ta tashi bayan da aka yada labarin cewa sojoji sun bude wuta a kan masu zanga zangar kin jinin rundunar SARS a unguwar lekki na birnin Logos a cikin watan da ya gabata.
Jami’an ‘yan sanda da dama ne suka bar wuraren ayyukansu bayan sun gano cewa wasu yansanda da dama suna nemansu don halakasu.(19)
342/