Mr. Johnson ya kasance jigo wajen ganin al’ummar Birtaniya sun kada kuri’ar ficewa daga kungiyar tarayyar Turai a zaben raba gardamar da suka kada a cikin watan jiya.
Mr. Johnson wanda tsohon magajin garin London ne, ya maye gurbin Philips Hammond wanda ya rike mukamin ministan harkokin waje a gwamnatin David Cameron.
To sai dai shi ma Hammond za a dama da shi a sabuwar gwamnatin, inda a yanzu May ta nada shi ministan kudi sakamakon goyon bayan da ya nuna mata.
Har ila yau, an nada Amber Rudd a matsayin ministan harkokin cikin gidan Birtaniya yayin da aka bar Michael Fallon akan mukaminsa na ministan tsaro.
Ana saran nan gaba kadan za ta nada ministocin lafiya da ilimi da kuma ayyuka da harkokin kasuwanci.288