Kwamishinan yada labaran jihar Ahmed Sajoh ya ce, cikin wadanda harin ya ritsa da su har da mata da kananan yara.
Wani babban jami’in hukumar bada aagjin gaggawa ta Najeriya a Yola, Sa’ad Bello ya tabbatar da mutuwar mutane 32 baya ga mutane 80 da suka jikkata a harin wanda ya auku da misalign karfe 8 da miniti 20 na dare agogon kasar.
Wata majiya ta ce, wani mutun ne ya je wajen yana raba kudi, abinda ya janyo hankulan mutane da dama kafin daga bisani aka tada dam din.
Harin dai ya yi kama da na kungiyar Boko Haram wadda a baya ta kai hare hare da dama a birnin na Yola.
Wannan dai na zuwa ne bayan Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira da ke samun mafaka a Yola, inda ya bayyana cewa an kusan kawo karshen kungiyar Boko Haram da ke tayar da kayar baya a Arewacin kasar. 289