Fadar shugaban na Amurka ta ce za a tura dakarun na musamman ne zuwa arewacin Syria domin bayar da horo ga ‘yan tawayen da Washington ke kira masu sassaucin ra’ayi da kuma hana yaduwar ayyukan kungiyar ISIS mai da’awar kafa daular musulunci a yankin.
Kakakin fadar shugaban na Amurka Josh Earnert, ya ce daukar wannan mataki ba wai yana nufin cewa kasar ta canza matsayin kan yadda take tafiyar da yaki a Syria ba ne. 289