A dai wajen Shugabannin za su tattauna kan batutuwan da suka shafi matsalar tattalin arziki,diflomasiya dama batutuwan kare hakin bil adam a kasar Masar.
Amurka na daya daga cikin mayan kasashe a Duniya dake bayar da gudunmuwa zuwa masar kan batutuwan da suka shafi tsaro,tareda bayar da horo zuwa dakarun Masar.
Akwai yiyuwar dai Sojojin Masar zasu kulla kawance da Amurka domin yakar Mayakan IS a Iraqi.
John Kerry bayan kasar Masar zai kai ziyara wasu kasashen Asiya dama yankin gabas ta tsakiya.288