Ranar Laraba 2 ga watan Zulqa’ada 1446 (30/4/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da Muballigai, wadanda Lujjanut Tablig ta shirya musu Mu’utamar na kwanaki uku a garin Suleja, a gidansa da ke Abuja.
A yayin jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara da taya murnar shiga watan Zulqa’ada, wanda a ranar 1 ga watan ne aka haifi Sayyidah Fatima Ma’asuma As, ‘yar Imam Musal Kazeem (AS), kuma a ranar 11 gare shi aka haifi yayanta, Imam Ali Bin Musar Ridha (AS), wanda Jagoran yace; “Saboda haka, wadannan ranaku tsakanin kwanakin nan 10 ana kiransu da ‘kwanuka 10 masu albarka”.
Da yake karfafa muhimmancin Tablig, Jagora (H) ya jaddada karantarwa a aji a matsayin mafificin hanyar yin Tabligi. Yace: “Ba wa’azi na gari ba, a karantar. Mutum ya zauna ya tankwashe kafa da littafi ya karanta littafin a makaranta. Ya zama akwai aji na yara, akwai ajin manya, wanda su manyan za su saka littafi ne, ba wai wa’azi (kawai za a yi musu su ji ba)”.
Jagora ya bayyana hanya ta biyu na Tabligi ita ce, isar da sako ta hanyoyin wa’azi. Inda ya bayar da misali da lokutan sallar Juma’a da akan je a kaddamar da huduba kafin ko bayan sallah, a yi magana da kowa da kowa, daidai gwargwadon fahimtar mutanen da suke muhallin. Yace: “Ba za a saka musu abinda fahimtarsu ba zai je gare shi ba, daidai fahimtarsu za a yi (magana da su)".
Shaikh Zakzaky (H) ya bayyana kafirta Musulmi da wasu sashin mutane suke yi a matsayin daya daga cikin makaman da aka kawo ma duniyar Musulmi na rusa ta. Yace: “Ina iya cewa ma, babban fitina da aka fuskanci wannan al’umma tamu, shi ne na ‘Takfiriyya’. Ba zan ce maka kungiya kaza, ko firka kaza, ko masu suna kaza ba, a’a, masu ra’ayin ce ma Musulmi kafiri. Wannan shi ne babban fitina da aka kawo mana.” Don haka, ya bukaci masu Tabligin da su rika magana da mutane akan abinda zai hade su waje guda ba tare da rarraba ba.
Shaikh Zakzaky, ya kuma jaddada bukatar ya zama Fudiyoyi sun tsayu akan hadafinsu, ba tare da an sauya suna ko manufarsu ba. Inda ya bayyana in wani na da ra’ayin samar da makaranta akan wani hadafi na daban, to ya samar don kansa, masu bukata su je, amma ba ya yi kokarin sauya hadafin makarantar Fudiyyah ba.
Yace: “Makarantar da muka yi na Fudiyyah ya zauna a zaman kansa. Shi yasa muka ce makarantar da muka yi muka saka masa Fudiyyah, muna nufin Fudiyanci ne. Fudiyanci kuma yana nufin tabbatan addini ne. Kuma sun san da wannan, shi ne abinda ba su so, hadafin nan. Don haka nake cewa, kar a manta da inda aka fito, da inda za a je”.
Jagora ya dauki lokaci yana bayani dangane da ma’anar Jihadi. Yace: “Ana cewa Danfodiyo, za su ce “Jihadi”. Har nakan ce ku gane fa, Jihadin nan ba yana nufin daukan takobi ba ne, yana farawa da kai kanka ne ka yi “jihadun nafs”, ka siffantu da addini tukunna, su ganshi a jikinka sannan kuma ka kira wasu”.
Yace: “Ko shi Shehu (da’awarsa) mataki-mataki ne, kamar yadda da’awar Manzon Rahma (S) ta kasance, da’awa ake yi. Shi yaki da takobin ya zo ne a karshe, ba takobi ne farko ba. To amma su suna cewa takobi ne. Takobin kuma ba da shi ya fara ba, an dira masa ne (ya kare kansa).
“Tamaman, Manzon Allah ai ya dauki takobi ko? Amma ba a Makkah ba, ba farkon al’amari ba, ko a Madina ma da aka biyo shi da yaki, an ta dauriya, suna cewa haka za mu zauna? Har sai da aya ta sauka “Uzina lillazina yuqataluna bi’annahum zulimu, wa innallaha ala nasrihim laqadir.” Har murna aka yi, sai da aka yi kiran sallah wanda ba a cewa ‘Hayya alas salah…’ Ana ta rungumar juna, (ana cewa:) Alhamdulillahi an ba mu izini (na kare kai).
“To amma sai da aka daure, aka daure, sai da ta kai ma lazim ne a kare kai. Ka ga daukan takobin ma a unwanin kare kai aka yi, ba unwanin kai hari ba. Ka ga yanzu wasu makiya suna ta fassara jihadi da cewa ana zuwa a dira ma mutum ne a kashe shi. In da shi Annabin nan (S) da ya zo da addinin nan, sai ya je da takobi ya sassare mutane, da ba su yi imani ba, - duk kafiran Makkah, to da wa zai yi imani? Ina addinin yake kenan?.
“Kai kana son ka cece mutum ne, ba ka halaka shi ba. Mutum in bai yi imani ba aka je aka kashe shi, an ingiza shi zuwa ga halaka kenan ko? To ai ana so a tsamar da shi ne, ba a halakar da shi ba. Wadanda suka hallaka kan su, su ne wadanda suka dauko takobi suka ce sai dai bayan ransu, amma sai sun ga bayan Annabi (S). To su ne a yunkurin wannan suka halaka. Kamar karon Badar wanda mutum sama da dubu cikin shirin yaki da makamai, suka fuskanci mutum 300 da ‘yan kai wanda ba su zo da shirin yaki ba, amma dai Allah Ya ba da nasara ga inda ya ba da nasara… A kokarin muttsike Annabi ne Allah Ya muttsike su, ka ga su suka muttsike kansu kenan”.
Har ila yau, Jagora (H) ya bayyana hanyoyin sadarwa da ake da su, inda akan yi rubutu, magana da sauransu a matsayin daya daga hanyoyin yin Tablig (isar da sako) idan an yi amfani da su a yadda ya dace.
Ya kuma ja hankali akan yadda ake yin raddi idan wani ya yi suka. Yace: “Na kan ga hujumi akanmu ya cika yawa yanzu, har nake cewa, to ba mu ce kar a yi raddi ba, amma don Allah ba radde-radde ya kamata a yi ba. Ya kamata idan ya zama wani ya sa ilimi da hankali ya yi magana, - ya yi raddi akan wani abu da aka yi, to ya wadatar, ba kowa kuma sai ya yi ba. In mutum daya ya bayar na hankali, kuma aka ji ya dace da hankali da ilimi (shikenan)”.
Yace: “Kuma hankali da ilimi za a sa (wajen yin raddin). Ko da mutumin da ya yi hujumin ya yi ashar da zage-zage, to ba zagin sa za a yi ba, ba kuma ce mishi za a yi ‘wawa’, ko wani abu ba, a’a ba zaginsa za a yi ba, za a ce ne, an ji wani Malami ya yi wata magana yace kaza-kaza, to ta yiwu haka aka fada masa, ko kuma haka ya karanta, to amma al’amarin ba haka yake ba, ga yadda yake”.
Dangane da yunkurin shigo da wasu da’awowi ta bayan fage, Jagora ya bayyana cewa: “Wadanda suke nan (kasar), da wadanda suke karatu a waje; Lebanon, Iraq, Iran, duk akwai da’awowi iri-iri, kowa da ra’ayinsa.” Yace: “Za ka ga Malaman da za su ce kawai gwagwarmaya bata lokaci ne, ga abinda za ka yi. Hatta ma wasu suna cewa, don me kuke sallar dare? Karatu ya kamata ku yi! Nace, za ka yi sallah, za ka yi karatu, daya baya hana daya, ni banga ta yadda mai karatu zai fasa sallah ba…”.
Yace: “Da’awowi kam ana yi mana su ko wane lokaci, saboda haka mutum ya lura kar a ja ra’ayinsa da kudi har ya zama ya kauce ma abinda ake kai.” Ya kara da cewa: “Shi yasa muka ce, ba mu ki mutum ya ba da gudummawa ba, amma kar yace mana ga abinda za a yi”.
A karshe, Shaikh Zakzaky ya ja hankali da cewa: “Ina nanata wa ‘yan uwa abu guda, kila ma su gaji da shi, amma dai abu guda ne cewa; na farko ka gyara kanka, a ga addinin daga wajenka, ya fi ma ka yi magana, sannan kuma ka koyar, sai ya zama kana koyarwa da dabi’a fiye da maganarka.
“Sannan kuma wani abu da nakan nanata shi ne Iklasi, Iklasi, yi don Allah, yi don Allah, yi don Allah. Don wa kake yi? Allah! In kana yin abu tsakaninka da Allah kake abinka, kar ka damu da sukan mai suka. Da yabon mai yabo, da sukan mai suka duk su zama tafiyarsu guda a wajenka. Ba ka yi don a yabeka ba, ba kuma za ka fasa don an soke ka ba, kana yi domin Allah ne, wannan yana da muhimmanci. Iklasin nan muhimmin abu ne”.
Sannan ya yi addu’ar Allah Ya cika burin ganin wannan al’umma ta sauya, ta dunkule ta zama abu guda, addini ya dawo ya yi iko da ita.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
02/Zulqada/1446
30/04/2025
Your Comment