Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya habarta cewa: Matakin da kasashen turai uku suka dauka na aiwatar da tsarin tunkarar Iran bisa umarnin Amurka ba zai haifar da komai ba illa dagula zaman lafiyar duniya. Tehran ta mayar da martani da kakkausan lafazi ga sanarwar da kasashen turai suka yi na cewa za su fara aiwatar da tsarin tunkarar Iran tare da fara samar da dokoki nan take na ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Dan majalisar dokokin kasar Iran Hussain Ali Haji Dalijani ya bayyana cewa, ana shirin gabatar da kudirin dokar dangane da hakan, wanda za a gabatar da shi a gaban majalisar a gobe. Wannan daftarin zai bi matakai na doka a cikin tarukan mako mai zuwa.
Ya ce wannan mataki na Jamus da Faransa da Birtaniya sun riga sun yi tsammaninsa kuma wannan ba wani sabon abu ba ne, illa dai tsohuwar dabarar da kasashen yammacin duniya suka dade suna amfani da su kan Iran.
Haji Dalijani ya ce babu amfanin tattaunawa da kasashen Turai, domin manufarsu ta ginu ne a kan ma'auni biyu kuma suna amfani da su a kan Iran a kowane lokaci.
Ya tunatar da cewa, a yayin da Iran ta shagaltu da tattaunawa da Amurka, haramtacciyar kasar ta sanya yaki a kan Iran sannan Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Wadannan al'amura sun tabbatar da cewa irin wannan tattaunawa bata lokaci ne kawai, don haka ya kamata a dakatar da tattaunawa da kasashen Turai.
Ya ce matakin da majalisar ta dauka na ficewa daga hukumar ta NPT martani ne kawai, sannan kuma za’a ci gaba da daukar tsauraran matakai domin kasashen Turai su yi nadama daga halinsu.
Your Comment