25 Afirilu 2025 - 22:19
Source: ABNA24
Zababbun Hadisai 20 na Imam Jafar Sadik (AS)

Imam Ja’afar Sadik (a.s.) yana cewa: “Hadisina hadisin babana ne, kuma hadisin babana hadisin kakana ne, kuma hadisin kakana hadisin Imam Husaini (a.s.), hadisin Imam Husaini As kuwa hadisin Imam Hasan (a.s.) ne, hadisin Imam Hasan (a.s) hadisin Amirul Muminin (a.s) hadisin Amirul Muminin (a hadisin manzon Allah (a.s.) ne, kuma hadisin manzon Allah (a.s.) maganar Allah ne madaukaki ne”.

Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.) yana cewa:

1. Hadisanmu hadisan annabci ne:

"حَدِيثِي حَدِيثُ أَبِي وَحَدِيثُ أَبِي حَدِيثُ جَدِّي وَحَدِيثُ جَدِّي حَدِيثُ اَلْحُسَيْنِ وَحَدِيثُ اَلْحُسَيْنِ حَدِيثُ اَلْحَسَنِ وَحَدِيثُ اَلْحَسَنِ حَدِيثُ أَمِيرِ اَلْمُؤْمِنِينَ عَلَيْهِ اَلسَّلاَمُ وَحَدِيثُ أَمِيرِ اَلْمُؤْمِنِينَ حَدِيثُ رَسُولِ اَللَّهِ صَلَّى اَللَّهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَحَدِيثُ رَسُولِ اَللَّهِ قَوْلُ اَللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ؛ (1)

Imam Ja’afar Sadik (a.s.) yana cewa: “Hadisina hadisin babana ne, kuma hadisin babana hadisin kakana ne, kuma hadisin kakana hadisin Imam Husaini (a.s.), hadisin Imam Husaini As kuwa hadisin Imam Hasan (a.s.) ne, hadisin Imam Hasan (a.s) hadisin Amirul Muminin (a.s) hadisin Amirul Muminin (a hadisin manzon Allah (a.s.) ne, kuma hadisin manzon Allah (a.s.) maganar Allah ne madaukaki ne”.

2. Falalar haddar hadisai arba'in

""مَنْ حَفِظَ مِنْ شِيعَتِنَا أَرْبَعِينَ حَدِيثاً بَعَثَهُ اَللَّهُ يَوْمَ اَلْقِيَامَةِ عَالِماً فَقِيهاً وَلَمْ يُعَذِّبْهُ؛  (2)

“Duk wanda ya haddace hadisai arba’in daga cikin mabiyanmu, Allah Ta’ala zai tayar da shi a ranar kiyama a matsayin malami kuma masanin fikihu kuma ba zai azabtar da shi ba”.

3. Ladan Biyan Bukatar Mumini ​​A Wurin Allah

"قَضَاءُ حَاجَةِ اَلْمُؤْمِنِ أَفْضَلُ مِنْ أَلْفِ حِجَّةٍ مُتَقَبَّلَةٍ بِمَنَاسِكِهَا وَعِتْقِ أَلْفِ رَقَبَةٍ لِوَجْهِ اَللَّهِ وَحُمْلاَنِ أَلْفِ فَرَسٍ فِي سَبِيلِ اَللَّهِ بِسُرُجِهَا وَلُجُمِهَا؛ (3)

"Biyan bukatur mumini ya fi Hajji dubu karbabbu, da 'yanta bayi dubu domin Allah, da nauyin kayan dawakai dubu tare da sirdodinsu da linzamansu a tafarkin Allah".

4. Abu Na Farko Da Ya Wajaba A Kiyaye Ita Ce Sallah.

"اَوَّلُ مايُحاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ الصَّلاةُ، فَاِنْ قُبِلَتْ قُبِلَ سائِرُ عَمَلِهِ، وَاِذا رُدَّتْ رُدَّ عَلَيْهِ سائِرُ عَمَلِهِ؛ (4)

“Sallah ce za a faraway bawa hisabi da ita a gaban Allah; "Don haka idan an karbe ta to za’a karbi sauran ayyukansa, idan kuma aka ki karbar sallarsa, to sauran ayyukansa ma ba za a karba su ba".

5. Halaye hudu da kira hudu a lokaci guda

"إِذَا فَشَتْ أَرْبَعَةٌ ظَهَرَتْ أَرْبَعَةٌ؛ إِذَا فَشَى الزِّنَا ظَهَرَتِ الزَّلازِلُ؛ وَإِذَا أُمْسِكَتِ الزَّكَاةُ هَلَكَتِ الْمَاشِيَةُ؛ وَإِذَا جَارَ الحُكَّامُ في القَضاءِ أُمسِكَ القَطرُ مِنَ السَّمَاءِ؛ وإِذَا خُفِرَتِ الذِّمَّةُ نُصِرَ المُشرِكونَ عَلى المُسلِمينَ؛ (5)

Idan a cikin al'ummar abubuwa hudu suka zama gama gari, to bala'o'i hudu za su dabaibaye wannan al'ummar: Idan zina ta zama ruwan dare, za a yawaita girgizar kasa; Idan aka ki fitar da zakka da Khumsi, dabbobin gida (kamar tumaki, awaki, rakuma, saniya, da sauransu) za su halaka; Idan har hukumomi da alkalai suka rungumi tafarkin zalunci a hukuncinsu, to za’a ki saukar da ruwan rahamar Ubangiji daga; "Kuma A duk lokacin da aka tauye zaman lafiya da tsaro, to mushrikai za su yi galaba a kan musulmi".

6. Hukuncin Aibata Dan Uwa Musulmi

"مَنْ عَابَ أَخَاهُ بِعَيْبٍ فَهُوَ مِنْ أَهْلِ اَلنَّارِ؛ (6)

"Duk wanda ya aibata dan'uwansa mumini da wani aibu, to shi dan wuta ne".

7. Amfanin Yin Shiru

"الصَّمْتُ كَنْزٌ وافِرٌ وَزَيْنُ الْحِلْمِ وَسَتْرُالْجَاهِلِ؛ (7)

"Shiru wata taska ce mai daraja, kuma adon hakuri da juriya ne, kuma hanya ce ta boye jahilcin jahili".

8. Sharadin Abota Da Zumunci

"إِصْحَبْ مَنْ تَتَزَيَّنُ بِهِ وَلا تَصْحَبْ مَنْ يَتَزَّيَنُ لَكَ؛ (8)

"Ka yi abota da wanda ya zame maka ado, kuma kada ka yi abota da wanda ya ke kawata maka".

9. Halaye Uku Wadanda Su Ne Silar Kamala Ga Mumini

"كَمالُ الْمُؤْمِنِ فى ثَلاثِ خِصالٍ: الْفِقْهُ فى دينِهِ وَالصَّبْرُ عَلَى النّائِبَةِ وَالتَّقْديرُ فِى الْمَعيشَةِ؛(9)

"Kamalar mumini tana cikin halaye guda uku: fahimta a cikin mas'alolin addini da hukunce-hukuncen addini, da hakuri da juriya a cikin wahalhalu, da tsarawa da tsantseni a cikin lamurran rayuwa".

10. Wajibci Da Falalar Halartar Masallatai

"عَلَيْكُمْ بِأَتْيَانِ الْمَسَاجِدِ فَإِنَّهَا بُيُوتُ اللَّهِ فِي الاَرْضِ ومَنْ أَتاها مُتَطَهِّراً طَهَّرَهُ اللَّهُ مِن ذُنُوبِهِ وكُتِبَ مِن زُوَّارِهِ فَأَكْثِرُوا فِيهَا مِنَ الصَّلَاةِ وَالدُّعَاءِ؛ (10)

Ya wajaba ku halarci masallatai, domin masallatai gidajen Allah ne a bayan kasa, kuma duk wanda ya halarci masallaci cikin tsarki, Allah Ta’ala zai tsarkake shi daga zunubansa, kuma ya sanya shi a cikin masu ziyartarsa. Don haka ku yawaita sallah da addu’a a cikin masallatai gwargwadon iko”.

11. Zikiri Na Musamman Bayan Sallar Asuba

"مَن قالَ بَعْدَ صَلوةِ الصُّبْحِ قَبْلَ انْ يَتَكَلَّمَ: "بِسْمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ وَلَاحَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إلَّا بِاللَّهِ الْعَليِّ الْعَظيمِ" يُعيدُها سَبْعَ مَرّاتٍ، دَفَعَ اللّهُ عَنْهُ سَبْعينَ نَوْعاً مِنْ أَنْوَاعِ الْبَلَاءِ، أَهْوَنُهَا الْجُذَامُ وَالْبَرَصُ؛ (11)

Duk wanda ya karanta “Bismillahir-Rahmanir-Rahim, La Hawla, La Quwwata Illa Billahil-Aliyil-Azeem” sau bakwai ba tare da ya ce komai ba bayan Sallar Asuba, Allah Ta’ala zai kare shi daga cututtuka iri 70, bala’o’i da musibu, mafi sauki kuma mafi kankantarsu ita ce kuturta.

12. Ladan Rashin Busar Da Baki Da Hannaye Bayan Alwala.

"مَنْ تَوَضَّأ وَتَمَنْدَلَ كُتِبَتْ لَهُ حَسَنَةٌ وَمَنْ تَوَضَّأ وَلَمْ يَتَمَنْدَلْ حَتّى يَجُفَّ وُضُوئُهُ، كُتِبَ لَهُ ثَلاثُونَ حَسَنَةً؛ (12)

"Wanda ya yi alwala ya busar da ita da tawul, to za’a rubuta masa kyakkyawan aiki guda daya, idan kuma bai busar da ita d atwul ba har sai da ta bushe da kanta, za’a rubuta masa kyawawan ayyuka guda 30".

13. Falalar Buda Baki A Gidan Dan Uwa Mumini

"لَاِفْطارُكَ فى مَنْزِلِ أَخيكَ أَفْضَلُ مِنْ صِيَامِكَ سَبْعينَ ضِعْفاً؛ (13)

"Bude bakin da za kai a gidan dan'uwanka mumini ya fi naka azumi sau 70".

14. Buda Baki Da Ruwan Zafi

"إِذَا أَفْطَرَ اَلرَّجُلُ عَلَى اَلْمَاءِ اَلْفَاتِرِ نَقَّى كَبِدَهُ وَغَسَلَ اَلذُّنُوبَ مِنَ اَلْقَلْبِ وَقَوَّى اَلْبَصَرَ وَاَلْحَدَقَ؛ (14)

"Idan mutum ya yi buda baki da ruwan zafi, hantarsa ​​za ta kasance mai tsarki da lafiya, za a wanke zuciyarsa daga zunubai, hasken idanuwansa kuma zai kara haske, ganinsa ya yi haske".

15. Fa'idodin Karatun Alqur'ani Yana Gabanka Da Idanunka

"مَنْ قَرَأَ القُرْآنَ فِي المُصْحَفِ مُتِّعَ بِبَصَرِهِ وَخُفِّفَ عَنْ وَالِدَيهِ وَإِنْ كَانَا كَافِرَينِ؛ (15)

Duk wanda ya karanta Alqur'ani mai girma da idanuwansa a bude zai amfanar da hasken idanuwansa kuma a sauƙaƙa daga zunuban mahaifansa biyu, ko da sun kasance kafirai".

16. Falalar Suratul Tauhidi

"مَنْ قَرَءَ قُلْ هُوَ اللّهُ احَدٌ مَرَّةً واحِدَةً فَكَانَّمَا قَرَءَ ثُلْثَ الْقُرآنِ وَثُلْثَ التُّوْرَاةِ وَثُلْثَ الإِنْجِيلِ وَثُلْثَ الزَّبُورِ؛ (16)

“Duk wanda ya karanta Qulhuwl Lahu Ahad sau daya: kamar ya karanta sulusin Alqur’ani da sulusin Attaura da sulusin Linjila.

17. Wanke Kayan Marmari Kafin Cin Su

"إِنَّ لِكُلِّ ثَمَرَةٍ سَمّاً فَإِذَا أَتَيْتُمْ بِهَا فَمَسُّوهَا بِالْمَاءِ أَوِ اغْمِسُوهَا فِي الْمَاءِ يَعْنِي اغْسِلُوهَا؛(17)

"Kowane 'ya'yan itace yana da nasa guba [kuma yana gurbata da kwayoyin cuta], don haka duk lokacin da ake son cin 'ya'yan itace, to ku wanke su da ruwa da farko, ko kuma ku dilmiya su a cikin ruwa, wato ku wanke su".

18. Amfanin turnips

"عَلَيْكُمْ بِالشَّلْجَمِ، فَكُلُوهُ وَأَدِيمُوأَكْلَهُ وَاكْتُمُوهُ إلَّا عَنْ أَهْلِهِ، فَمَا مِنْ أَحَدٍ إلَّا وَبِهِ عِرْقٌ مِنَ الْجُذَامِ، فَأَذِيبُوهُ بِأَكْلِهِ؛(18)

Ku yawaita anfani da ƴaƴan turnips, kuma ku dimanci cin su, kuma ku ɓoye shi sai ga wanda suka cancanta (fa'idodinsu daga jahilai) domin kowane mutum yana da jijiyar kuturta, don haka ku kawar da ita ta hanyar cin 'ya'yan itace turnips".

19. Gurare Hudu Da Ake Karbar Addu’a

"يُسْتَجَابُ اَلدُّعَاءُ فِي أَرْبَعَةِ مَوَاطِنَ فِي اَلْوَتْرِ وَبَعْدَ اَلْفَجْرِ وَبَعْدَ اَلظُّهْرِ وَبَعْدَ اَلْمَغْرِبِ؛ (19)

"Ana amsa addu'a a gurare hudu: a lokacin sallar witiri (a cikin Tahajjud), da bayan sallar asuba, da bayan sallar Azuhur, da kuma bayan sallar magriba".

20. Falalar Yin Addu’a A Daren Juma'a Ga Matattu 10 Muminai

"مَنْ دَعا لِعَشْرَةٍ مِنْ اخْوانِهِ الْمَوْتى لَيْلَةَ الْجُمُعَةِ اوْجَبَ اللّهُ لَهُ الْجَنَّةَ؛

"Duk wanda ya yi addu'ar gafara ga Yan uwansa muminai guda 10 da suka rasu a daren Juma'a, Allah Ta'ala zai wajabta masa Aljanna".

______________________________________________________________________________________________________________________________________________________________

[1]۔ الکلینی، محمد بن یعقوب الرازی، الکافی، ج1، ص53۔

[2]۔ الشیخ الصدوق، محمد بن علی، الامالی، ص253.

[3]۔  الطبرسی، علی بن حسن بن فضل طبرسی (سبط امین الاسلام)، مشکاۃ الانوار فی غُرَرِ الاخبار، ج1، ص148۔

[4]۔ الحرالعاملی، محمد بن حسن، وسائل الشیعہ، ج3، ص22۔

[5]۔ الشیخ الصدوق، من لا یحضرہ الفقیہ، ج1، ص524۔۔

[6]۔ الشیخ المفید، مجمد بن محمد العکبری، الاختصاص، ص240۔

[7]۔ البحرانی الاصفہانی، عبداللہ بن نور اللہ، ج20، ص779؛ النوری الطبرسی، حسین بن محمد تقی، مستدرک الوسائل و مستنبط المسائل، ج9، ص16۔

[8]۔ الطبرسی، حسن بن فضل، (امین الاسلام کے فرزند)، مکارم الاخلاق، ج1، ص251۔

[9]۔ الشیخ الطوسی، محمد بن حسن، الامالی، ص666؛ الطبرسی، علی بن حسن، مشکاۃ الانوار فی غُرَرِ الاخبار، ج1، ص278۔

[10]۔ الشیخ الصدوق، الامالی، ص440۔

[11]۔ الشیخ الطوسی، الامالی، ص415۔

[12]۔ الکلینی، الکافی، ج3، ص70۔

[13]۔ الشیخ الصدوق، من لايَحضرہ الفقيہ، ج2، ص51۔

[14]۔ الکلینی، الکافی، ج4، ص152۔

[15]۔ الکلینی، الکافی، ج2، ص613۔

[16]۔ الشیخ الصدوق، التوحید، ص95۔

[17]۔ الکلینی، الکافی، ج6، ص350۔

[18]۔ الطبرسی، حسن بن فضل، مکارم الاخلاق، ج1، ص207۔

[19]۔ ابن فہد حلی، أحمد بن محمد، عدۃ الداعی و نجاح الساعی، ج1، ص67۔

[20]۔ الحر العاملی، وسائل الشیعہ، ج2، ص124۔

Your Comment

You are replying to: .
captcha