10 Afirilu 2025 - 11:35
Source: ABNA24
Ayatullah Faqihi: Muhimmancin Rikon Amana A Ayyukan Kafafen Yada Labarai.

Ayatullah Faqihi Memba na kungiyar malaman makarantar Qum ya jaddada muhimmancin rikon amana a ayyukan kafafen yada labarai a yayin ziyartarsa kamfanin dillancin labarai na ABNA

A yayin da yake ishara da muhimmancin rikon amana a kafafen yada labarai, Ayatullah Faqihi ya bayyana cewa: Idan muka ci gaba da rike gaskiya da rikon amana a fagen magana da yada labarai, to za mu iya samar da ayyuka masu girma.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As – ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Muhsin Faqihi mamba na kungiyar malamai ta Qum, ya ziyarci ofishin gudanarwa na kamfanin dillancin labarai na ABNA, inda ya yi masa bayani kan ayyukan Kamfanin.

Bayan kammala wannan ziyara, Ayatullah Faqihi ya halarci wani taro da manema labarai na wannan kamfanin dillancin labarai, inda a jawabin da ya gabatar ya bayyana manufofin kafafen yada labarai a halin da ake ciki da kuma muhimmancin kyakkyawar halayya a cikin aikin jarida.

Wannan memba na kungiyar malaman makarantar Hauzar Qom, a jawabinsa na yabawa da ayyukan da aka yi, ya yi jawabi ga manema labarai na wannan kamfanin dillancin labarai, ya kuma ce: “Kamfanin dillancin labarai na ABNA yana ba da hidimomin da suka dace da yaruka daban-daban, kuma wadannan ayyuka sun cancanci girmamawa da godiya.

Malamin makarantar hauza na Qum ya ce: Dole ne mu kasance da niyyar kusantar mutane a cikin ayyukanmu. Lallai ne mu sani cewa duk abin da muke da shi daga Allah yake kuma mu kasance masu tsayin daka a tafarkin Allah.

Wannan memba din kungiyar malamai ya bayyana cewa: “Kowace kalma da muka rubuta dole ne ta zama mai faranta wa Allah da kuma Imamin lokacin (a.t.f.) dadi, mu bi tafarkin da Imamin zamani (a.s) ya yarda da shi kuma Jagora ya yarda da shi.

A yayin da yake ishara da muhimmancin rikon amana a kafafen yada labarai, Ayatullah Faqihi ya bayyana cewa: Idan muka ci gaba da rike gaskiya da rikon amana a fagen magana da yada labarai, to za mu iya samar da ayyuka masu girma.

A farkon wannan ziyarar, Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, Hasan Sadrai Arif, ya gabatar da rahoton ayyukan ma’aikatu daban-daban na Kamfanin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha