6 Afirilu 2025 - 18:13
Source: ABNA24
Lamarin Maqabartar Al-Baqih Ya Zamo Rauni A Cikin Zuciyar Al'umma Kuma Tuta Da Ba Za Ta Fado Ba.

Al-Baqi' Al-Gharqad ita ce makabartar Musulunci mafi tsufa kuma mafi tsarki, wacce ke dauke da gawarwakin wasu manya-manyan mutane wadanda suka gina tarihin al'umma. A nan ne aka binne Imaman Ahlulbaiti hudu (Imam al-Hasan al-Mujtaba (a.s) da Imam Zainul Abidin (a.s) da Imam Muhammad al-Baqir (a.s) da Imam Ja’afar al-Sadik (a.s), baya ga dimbin sahabbai, uwayen muminai da tabi’ai da malamai masu yawa wadanda suka bar gudunmawa da ba za’a iya share ta ba.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa, a tsawon tarihi, a akwai wasu gabobi na tarihi wanda ba wai kawai abubuwa ne da suka faru kwatsam suk wuce ba kawai, sai dai hakan ya koma wata gaba mai muhimmanci ga ga fahimtar gama-garin al'ummar musulmi. Domin wadannan waki’oi suna bayyana yanayin gwagwarmayar da ke tsakanin haske da duhu, tsakanin kiyaye ingantaccen gadon Musulunci da yunkurin shafe shi da gurbata shi. Daga cikin waxannan abubuwa, akwai abun da ya faru ranar takwas ga watan Shawwal, ta zo ne domin tunatar da mu musibar da ta faru na rushe kaburburan Imaman Baqi’ (amincin Allah ya tabbata a gare su), Ta’addancin da tasirinsa bai gushe daga tunanin musulmi ba, sai dai ya zama shaida kan harin mai gauni da aka kai kan alamomi da alfarmar Musulunci.

Al-Baqi' Al-Gharqad ita ce makabartar Musulunci mafi tsufa kuma mafi tsarki, wacce ke dauke da gawarwakin wasu manya-manyan mutane wadanda suka gina tarihin al'umma. A nan ne aka binne Imaman Ahlulbaiti hudu (Imam al-Hasan al-Mujtaba (a.s) da Imam Zainul Abidin (a.s) da Imam Muhammad al-Baqir (a.s) da Imam Ja’afar al-Sadik (a.s), baya ga dimbin sahabbai, uwayen muminai da tabi’ai da malamai masu yawa wadanda suka bar gudunmawa da ba za’a iya share ta ba.

Al-Baqi'i ba wai makabarta ce kawai ba, a'a, wata fitila ce ta ruhi da tarihi, inda muminai daga dukkan mazhabobin Musulunci su ke tururuwa don ziyartar ta, suna neman albarka da tunawa da rayuwar manyan mutane da aka binne a wurin. To sai dai wannan alama da guri mai tsarki da ta hada kan musulmi daga kowane bangare, ta fuskanci mummunan hari a shekara ta 1344 bayan hijira (1926 miladiyya) a lokacin da mahukuntan wahabiyawa suka ruguza matattarar ta, suna masu fakewa da akida mai tsauri da ke kin girmama waliyyai salihai da daukar ziyarar kaburbura wani nau'i ne na shirka.

Harin Baqi’i da aka maimaita shi: Rusa Alamin Baki’a sau biyu aka yi wanda Rushewar ranar takwas ga watan Shawwal 1344 ba ita ce irinsa na farko ba. Sai dai, wani ta’addancin ya faru a shekara ta 1220 bayan Hijira, lokacin da mabiya Wahabiyawa suka mamaye iko da Madina a karon farko.

A lokacin ne aka rusa kaburburan mutanen Baqi tare da tone su, sannan barnar bata tsaya anan ba ta kai har da kabarin Annabi Muhammad (SAW) da kansa, idan da ba don anyi ta kiray-kiraye ba da manyan muryoyin adawa da yin zanga-zangar nuna fushi daga sassa daban-daban na duniyar Musulunci.

A shekara ta 1233 bayan da Daular Usmaniyya ta sami nasarar karbe ikon yakin Hijaz, an sake gyara kaburburan Baqi'a, aka gina sabbin qubbobi da manyan wurare ibada a ciki. Wadannan alamomin sun kasance a karkashin kulawarsu har zuwa farkon karni na sha hudu bayan hijira.

To sai dai kuma bayan faduwar daular Hijaz a hannun Abdul Aziz bin Saud, tare da goyon bayan Birtaniyya, sannan kuma da hadin kan kawancen siyasa da akida a tsakanin gidan Al-Saud da Wahabiyawa, an sake aiwatar da aikin rushewar da sunan fakewa da “hada kan ibada” da kuma hana yin bidi’a. An lalata kaburbura, an kwashe dukkan qubbobin, an wawashe dukiyoyi, an kuma kafa wani tsatstsauran hangen nesa na addini ta hanyar amfani da makamai.

Amma abu mafi ciwo wannan ta’addancin guda biyu shi ne, ya faru ne a cikin yin shiru na duniya, inda gwamnatocin Musulunci suka yi shiru, duk kuwa da barkewar zanga-zangar da jama'a suka yi a kasashen Iran, Iraki, Indiya, da sauran sassan duniyar Musulunci.

Har ila yau, abin lura shi ne, daga cikin kaburburan da su ma aka rusa akwai haramin Sayyidah Fatima bint Asad, mahaifiyar Imam Ali (a.s), da haramin Ibrahim dan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), da kaburburan da aka jingina ga matan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda hakan ke nuna irin girman barnar da aka yi kan alamomin Musulunci na duniya da musulmi ba su bambanta ba wajen girmama su.

Martanin malamai da sauran jama'a Da labarin rugujewar ya bazu, sai guguwar bakin ciki da bacin rai suka mamaye duniyar Musulunci. Muryoyin malamai a Najaf da Kum da Karbala sun tashi suna kira ga musulmi da su tinkari wannan karkacewar. Manyan hukumomin addini irin su Sheikh Naini, Akhund Khorasani, Sayyid Shirazi ne suka fitar da jawabai masu kakkausar murya, inda suka yi Allah wadai da wannan zalunci.

An kuma gudanar da zanga-zangar a biranen Bagadaza, Tehran, Mashhad, Lucknow, da Indiya, tare da daga tutoci na yin Allah wadai da shirun Larabawa da na Musulunci a hukumance tare da yin kira da a sake gina kaburbura da kuma kiyaye wurare masu tsarki.

Abun da rushe Al-Baqi'a ke nunawa shi ne: Wannan mummunar ɗabi'a ta ɓarna ba wai kawai an nufi gurare ne na gininnikan addini ba a'a har ma an nufaci rushe ruhin Musulunci da kuma yin aiki don shafe ƙwaƙwalwar ruhin al'umma. Makabartar Baqi' tare da abin da ta ke dauke da shsi na alamomin musulunci, tana wakiltar fuska mai rai na tarihin Musulunci, tana mai hada hikimar Annabci da imamanci, jihadi na ilimi da jihadi na zamantakewa, da sahabbai muminai da tsarkakan iyalan gidan manzon Allah.

Don haka rusa ta wani yunƙuri ne na kawar da wannan ruhiyya da kuma keta lamirin Musulunci na cibiyoyin masu tasirin da haskaka tunani. Don haka kare alfarmar Baqi'i da neman sake gina ta kariya ce ba da haqiqanin kariya ce ga ma'anar gadon Musulunci da kuma watsi da tsarin akidar da ke kokarin ganin an takure Musulunci zuwa ga kuntatacciyar fahimta mai tsauri.

Muhimmancin tunawa da ranar takwas ga watan Shawwal Ranar takwas ga watan Shawwal ba wai kawai ranar makoki ba ce, a'a ranar fadakarwa ce da yunkuri da motsawa. Tunawa da wannan zagayowar ya zama wajibi ga duk musulmin da ya girmama huruminsa, domin ya tabbatar da cewa ba za a taba mantawa da wannan laifi ba, kuma ba za a shafe tasirinsa ba. A maimakon haka, zai kasance shaida ne ga yunƙurin gurɓatawa da karkatar da hakikanin Musulunci a tsawon tarihi.

Tuna da wannan rana bai kamata a takaitu ga zaman makoki da zaman makoki ba, a'a, ya zama wani lokaci na sake farfado da batun Baqi'a a fagen Musulunci da na kasa da kasa, da neman hakkin musulmi na sake gina wadannan wurare masu tsarki.

Nauyin da ya hau kan musulmi dangane da Baqi'i:

Nauyin musulmi dangane da al'amarin Baqi' bai tsaya a kan tofin ala tsine da tsinewa wadanda suka keta huruminta ba, a'a yana bukatar yin yunkuri da aiki mai tsanani don cimma manufofinsa: 

1. Watsawa da fadakarwa kan matsayi da tarihin makabartar Baqi': Malamai da masu tunani su fitar da bincike da kasidu da ke nuna muhimmancin wannan wuri a tarihin Musulunci. Sannan su yi karin haske kan tarihin limaman da aka binne a wurin da irin rawar da suke takawa wajen raya al'ummar musulmi.

2. Neman sake gina makabartar Baqi'a: Dole ne a samu wani yunkuri na kasa da kasa na neman hakkin musulmi na sake gina wannan wuri mai tsarki, kamar yadda ake girmama alfarmar mabiya sauran addinai a duniya. Haka nan kuma dole ne a kafa kwamitocin kare hakkin bil'adama da na addini domin tada murya a tarurrukan kasa da kasa domin dakile hare-haren da ake kai wa wuraren da addinin Musulunci ya tanada.

3. Karfafa hadin kan musulmi a kan wannan mas’alar: Al-Baqi’ ya kamata ta zama wani abu mai tasiri na hadin kan musulmi, ba rarrabuwar kawuna ba, domin dukkan musulmi suna darajja iyalan gidan manzon Allah (saw) da sahabbansa madaukaka. Haka nan kuma ya kamata a gudanar da taruka da tarukan karawa juna sani a duniya, domin tattaunawa kan girman wannan laifi da tasirinsa ga al'ummar musulmi.

4. Saka hannun jari a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta don yada labarai: Ya kamata a sadaukar da shirye-shiryen Documentary da kasidu na lokaci-lokaci wajen ba da labarin Al-Baqi’ da hare-haren da aka kai. Ya kamata kuma a shirya fina-finai da shirye-shiryen bidiyo don bayyana mahimmancin Al-Baqi’ da kuma rubuta buƙatun musulmi na sake gina sh

Rushe Baqi'a ba wai kawai lalata duwatsu ba ne, a'a hari ne kan tunani da fikira da ruhiyyar al'umma da kuma addininsu. A yau wajibi ne ga kowane musulmi kada ya manta da wannan musiba, ya kuma yi kokarin gyara wannan zalunci na tarihi.

Tunawa da ranar takwas ga watan Shawwal, farfaɗo da adalci na tarihi, kiyaye mutuncin Musulunci, da yin kira don maido da abin da aka sace daga tsarkakan wuraren musulmi. Wannan aikin ba zai cika ba har sai mun ga makabartar Baqi’i tana haskakawa kamar yadda take, tana mai nuna girman Musulunci da dauwamar da alamominsa, da kuma tsayawa a matsayin shaida cewa gaskiya komai yakar ta da za’ai ba ta mutuwa ko an manta da ita.

Your Comment

You are replying to: .
captcha