Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA — bisa nakaltowa daga Kamfanin labaran IRNA cewa, Amurka ta kai hari a yankin da ke kusa da birnin Saada na arewacin kasar Yemen sau biyu a yau Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta bisa nakaltowa daga shafin yada labarai na Al-Mayadeen cewa bai bayar da wani karin bayani kan wannan labari ba, ko kuma hasarar da aka yi samu acikinsa ba.
A baya dai jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a wasu yankunan lardin Saada da ke arewacin kasar Yemen a safiyar Asabar da kuma daren Juma'a.
Jiragen yakin Amurka sun yi ruwan bama-bamai a lardin Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen a yammacin ranar Alhamis.
A ranar Talata ma jiragen yakin Amurka sun kai hari a yankin Takhiya da ke birnin Majaz na lardin Saada a lokuta da dama.
A baya dai ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana hare-haren da jiragen yakin Amurka da na Birtaniyya suka kai kan wasu unguwanni a birnin Sanaa a matsayin wani aiki na kiyayya da kuma aikata laifukan ta'addanci.
Dakarun kasar Yemen sun jaddada cewa, za su ci gaba da tinkarar hare-haren wuce gona da irin na Amurka da kuma hana zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra'ila har sai an daina kai hare-hare a zirin Gaza gaba daya, tare da kawo karshen mamaye yankin.
Your Comment