22 Maris 2025 - 08:05
Source: ABNA24
Allamah Sheikh Zakzaky {H}: Zaluntar Rarrauna; Shi Ne Zaluncin Da Ya Fi Muni

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin sharhin Tafsirin Suratul Ma'un ya bayyana cewa: “Zaluntar rarrauna shi ne zaluncin da ya fi muni, na'am duk zalunci bashi da kyau, duk zalunci zalunci ne, amma ana iya zaluntar Sarki a ƙi bashi haƙƙinsa, ko ba haka bane? Har Mawadaci ma ana iya zaluntarsa, duk wanda aka hana shi haƙƙinsa ai an zalunci shi. To zaluncin da ya fi muni shi ne zaluntar rarrauna. Galiba ma mu in mun ce zalunci abin da muke tunani kenan, ana nufin rarrauna aka zalunta. Amma kun ga Amirulmuminina ya nuna ana zaluntar sa, gashi shi yana rabawa Mutane komai, shi bai ɗauki kayansu ya fifita da shi ba, yana musu komai, amma sun ƙi su bishi, wato sun zalunce shi a haƙƙinsa na biyayya. 

“Imam Ali yana cewa “sauran shuwagabanni talakawansu na kuka akan shuwagabanninsu na zaluntarsu, Ni kuwa ina kuka akan cewa Talakawana na zalunta ta”, saboda shi ya musu abin da ya kamata amma su sun ƙi bashi nasa haƙƙin, to ka ga sun zalunce shi. To wanda ya fi muni shi ne zaluntar rarrauna.

“Yazo a cikin Hadisi cewa: “Wanda ya taimaki azzalumi, kuma ya san shi azzalumi ne, to ya kuɓuta daga Musulunci” Wato ya fita daga Musulunci, ma'ana ya yi baran-baran da Musulunci, wanda ya taimaki azzalumi kuma ya san shi azzalumi ne. A wannan ma'anar ya nuna cewa shi azzalumi a ranar Lahira za a masa mu'amalar Kafiri ne,   domin ita wannan aya ta gwama zaluntar Maraya da kuma ƙaryata addini, (kar kuma ka ce masa Kafiri) Idan azzalumi ya yi shahadataini wato ya furta ‘La'ilaha Ilallalah Muhammadu Rasulullah’ a duniya za a masa mu'amala irin na Musulmi ne, amma a Lahira waɗannan ‘La'ilaha Ilallalah Muhammadu Rasulullah’ ɗin ba za su tsinana masa komai ba, hatta koda ya yi Sallah, ya yi Azumi, ya yi Hajji. Wannan ba ra'ayina nake karanta muku ba, ina karanta muku daga littafi ne, ra'ayin wani ne. Ka ga wannan ta nuna cewa wanda yake cin zalin Maraya shi bai yi imani ba.

“In ka ce deen sakamako ne ‘yes’ haka ɗin ne, amma ya ƙaryata sakamako, shi a nan bai yi aikin da zai samu a can ba. Mun sha kuma faɗan cewa; shi Imani  yana ɗamfare ne da aikin kirki, Imani ba aikin kirki, ba ya tsinana ma mai imanin komai. Ran da ba ta yi aikin kirki ba imaninta ba zai tsinana mata komai ba, ko kuma wanda ta yi imani ba ta yi aikin alheri ba. To shi wannan imani shigen irin wannan, shi ne kamar wanda ba ta aikata alheri ba wanda ba zai tsinana masa komai ba.

“Na'am a nan tana iya yiwuwa ya gina Masallaci, ko ba haka bane? Ya sa mishi darduma, ya zo ya riƙa yin wasu abubuwa, ya zo a yi Sallah da shi, amma dai haƙƙoƙin Mutane ya tattara ya bar su cikin Talauci, koda kuwa yana ɗan ɓantarowa ya bada waɗansu daga cikinsu”.

Nakaltowa Daga: Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky 

22 Ramadan 1446 (22/3/2025)

Your Comment

You are replying to: .
captcha