21 Maris 2025 - 05:12
Source: ABNA24
Gagarumar Zanga-Zangar Aka Tel Aviv Da Jerusalem Na Neman Kawo Ƙarshen Yaƙi Da Musayar Fursunoni 

Rikici ya barke tsakanin sojojin yahudawan sahyoniya da masu zanga-zangar yahudawan sahyoniya a Tel Aviv 

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait (As) -Abna- ya habarto maku cewa: Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, daruruwan mutane a birnin Tel Aviv sun gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen yakin, da komawa kan teburin tattaunawa, da kuma gaggauta sakin fursunonin Isra'ila dag Gaza.

A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gudanar da irin wannan zanga-zanga a birnin Kudus da aka mamaye domin nuna adawa da korar shugaban Shin Bet da aka yi da kuma neman kawo karshen yakin Gaza.
Jaridar Haaretz ta Sahayoniyya ta bayar da rahoton cewa, 'yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zangar bayan da suka yi kokarin isa gidan Netanyahu da ke birnin Kudus ta hanyar tsallaka shinge.
Haaretz ya ba da rahoton adadin masu zanga-zangar da ɗaruruwa kuma sun ba da rahoton cewa suna shirin ci gaba da kasancewa kan tituna a cikin kwanaki da makonni masu zuwa tare da ci gaba da zanga-zangar adawa da Netanyahu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha