21 Maris 2025 - 04:43
Source: ABNA24
Bidiyo Yadda Tankunan Sojojin Isra'ila Ke Shiga Gaza

Tankunan sojojin Isra'ila sun shiga zirin Gaza domin ci gaba da yaƙin kasa gaba da gaba tare Dakarun gwagwarmaya

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait (As) -Abna- ya habarto maku cewa: Sojojin Isra'ila sun fara kai farmaki ta kasa a arewaci da kudancin Gaza

Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kaddamar da hare-hare ta kasa a kudanci, da tsakiya, da kuma arewacin zirin Gaza. A cewar wani rahoto da gidan talabijin na Channel 12 na Isra'ila ya bayar; Sojojin sun shiga yankunan arewacin zirin Gaza a karon farko tun bayan tsagaita bude wuta.
Rundunar ta jaddada cewa za ta fadada ayyukanta na soji na kasa tare da sake kwato wasu yankunan da suka kuɓuta a lokacin da aka tsagaita bude wuta.
Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa tana kokarin fadada yankin tsaro bayan da ta kwace iko da yankin Netzarim da ke tsakiyar zirin Gaza.
Sojojin gwamnatin kasar sun kuma haramta zirga-zirgar Falasdinawa a kan titin Salahad-Din tsakanin arewaci da kudancin Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha