20 Disamba 2024 - 13:32
Adadin Shahidai A Zirin Gaza Ya Karu Zuwa Mutane 45,206

Adadin shahidai a Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai dubu 45 da 206 sannan adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa mutane dubu 107 da 512.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) – ABNA – ya habarta maku cewa: ma’aikatar lafiya ta yankin Gaza ta sanar da samun karuwar shahidai a wannan yanki tun bayan fara yaki da yahudawan sahyuniya a ranar 7 ga watan Oktoba, inda adadin ya kai 45,206 wadanda suka jikkata zuwa mutane 107,512. 

Ma'aikatar ta kara da cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata gwamnatin yahudawan sahyuniya ta aikata laifukan kisan gilla guda uku a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda mutane 77 suka yi shahada tare da jikkata wasu 174.

A cewar jami'an ma'aikatar lafiya ta zirin Gaza har yanzu da yawan gawarwakin shahidan na karkashin baraguzan gine-gine ko kuma jibge a kan tituna, kuma masu aikin ceto da na jama'a ba sa iya taimakawa wadanda suka jikkata.

...................................