12 Disamba 2024 - 11:55
Jagora: Da Yardar Allah Gwagwarmaya Za Ta Kori Amurka Daga Yankin Gabas Ta Tsakiya

Shi dai wancen jahili manazarcin da bai san ma’anar gwagwarmaya ba, yana ganin cewa idan aka raunanar da gwagwarmaya to Iran din Musulunci ma za ta yi rauni! Ina mai cewa Iran tana karfi da iko kuma za ta kara karfi da izinin Allah.

Na fada cewa "fagen gwagwarmaya" bari in fadi wasu 'yan kalmomi game da "fagen gwagwarmaya". Wakilan ma'abota girman kai sun yi farin ciki bayan wadannan abubuwan da suka faru a Siriya, suna bayyana farin cikinsu suna tunanin cewa bayan faduwar gwamnatin Siriya, wacce ke goyon bayan gwagwarmaya, bangaren gwagwarmaya ya yi rauni. Suna murna suna cewa gaba dayan gwagwarmaya ta yi rauni; A ganina sun yi kuskure sosai. Wadanda suke ganin an raunana bangaren gwagwarmaya da faruwar wadannan abubuwa, to ba su da kyakkyawar fahimtar ga gwagwarmaya da fagen gwagwarmaya; Ba su san me ake nufi da gwagwarmaya ba.

“Fagen gwagwarmaya” ba kayan aiki na jiki ba ne wanda zai karye ko ya fado ko ya lalace. “Tsarin gwagwarmaya” imani ne, tunani ne, zuciya ce kuma tabbataccen qudiri ne; gwagwarmaya makaranta ce, makarantar imani. Abunda ya ke Imani ne na wasu mutane, ba abu ne na al'ada ba - wanda a yanzu nake cewa to me ya sa zama imanin mutane ne – wannan imanin ba wai kawai ba ya raunana ba ne ta hanyar kuntatat ma a’a ta hakan yana kara samun karfi ne.

Burin ma'abota gwagwarmaya da jigogin gwagwarmaya na kara karfi ne ta hanyar ganin munanan ayyukan makiya kuma ta hakan fagen gwagwarmaya yake kara fadada. Lokacin da suka ga munanan laifukan makiya, wadanda suke shakkar ko za su yi gwagwarmaya ko a'a, sai su fito daga cikin shakku, su fahimci cewa, sai dai ta hanyar bayar da kare kirji agaban azzalumi, mutum ba zai iya ci gaba da tafiyarsa akan tafarkinsa ba; dole ne ya tsaya, dole ne yayi gwgwarmaya; gwagwarmaya tana nufin wannan ne.

Ku dubi kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, ku dubi Hamas, ku dubi Jihad, ku dubi dakarun Palastinawa masu gwagwarmaya; dukkansu sun takura masu ne sosai. Shin musibara da ya afkawa Hizbullah abin wasa ne? Hizbullah ta rasa mutum kamar Sayyid Hasan Nasrallah; shin wannan karamin abu ne? Hare-haren Hizbullah, da karfin Hizbullah, hare-haren masu karfi ya zarce a da bayan faruwar hakan; Su ma makiya sun fahimci hakan kuma sun yarda da hakan. Sun yi tunanin cewa yanzu da suka kai hari, za su iya shiga cikin kasar Labanon, su kori Hizbullah, misali, zuwa kogin Litani, ya zamo sun kara yin gaba; ammam ba su iya zuwa. Hizbullah ta tsaya da cikakken iko; Ta yi wani abu da su da kansu suka zo suka ce: a tsagaita wuta! Wannan ita ce gwagwarmaya.

Ga dubi Gaza! Sun shafe shekara guda da ’yan watanni suna kai hare-haren bam a Gaza. sun kasha mutane zabbabu misali Yahya Sinwar suka shahadantar da shi, sun wannan mumman aiki. A lokaci guda kuma mutane sun jajirce sun tsaya kyam, sun yi tsammanin za su matsa wa mutane lamba don su da kansu su tashi su yaki Hamas; amma sai sabanin hakan ya faru; Mutane suka zama masu goyon bayan Hamas. Haka Jihadi ya ke, sauran al'ummar Palastinu suma haka suke, wannan si ake ira gwagwarmaya, fagen gwagwarmaya hakanan ya ke: da zarar an matsa masa, a sa’ilin yake ƙara ƙarfinsa; Duk yadda kuka kai da aikata laifin ta’addanci, gwagwarmaya tana kara kaimi ne, duk yadda kuka kai kuna yaki da ita ita kuwa tana kara fadada ne. Kuma ina mai fada muku, da ikon Allah, gwagwarmaya zata kara girmama a yankin ta mamaye shi baki daya fiye da a baya. Shi dai wancen jahili manazarcin da bai san ma’anar gwagwarmaya ba, yana ganin cewa idan aka raunanar da gwagwarmaya to Iran din Musulunci ma za ta yi rauni! Ina mai cewa Iran tana karfi da iko kuma za ta kara karfi da izinin Allah.

Bari in sake faɗi wani abu game da gwagwarmaya. Yanzu dai da farko, bari in gaya muku ma'anar hakika ta gwagwarmaya. Gwagwarmaya na nufin tsayuwa kyam agaban mamayar Amurka da duk wani mai mulki; Wannan ita ce ma'anar gwagwarmaya. Gwagwarmaya na nufin yaki da masu dogaro da wadannan masu mulkin; gwagwarmaya tana nufin al'ummomi ka da su zama bayin manyan kasashe kamar Amurka da makamantansu; Wannan ita ce ma'anar gwagwarmaya. Gwagwarmaya a wannan ma'ana ta samo asali ne daga imanin al'ummomin yankin. Ba ruwa na da gwamnatoci; Al’ummu suke bawa gwagwarmaya mahimmanci; Tushen gwagwarmaya yana cikin imanin al'ummomi da abunda suka yarda da shi. Shin kun ga abin da al'ummomin yankin suka yi game da [goyon bayan] Gaza? Wadanda ba su jin yarensu, ba su ga yankinsu ba, ba su san su da kansu ba, a duk fadin wannan yanki - a yanzu a duk fadin duniya - sun yi tsayin daka wajen adawa da gwamnatin sahyoniyawan da kuma amfanar al'ummar Gaza. Wannan ita ce akidar gama-gari na kasashen yankin, kuma saboda wannan dalili dayan ne.

Kun ga kusan shekaru 75 kenan da mamayar Falasdinu; To, abin da ya faru shekaru 75 da suka gabata, ya kamat ace a hankali ya dushe, har mutane su manta, su yi shiru. A yau matsayin da al'ummomin yankin da su kansu Palasdinawa suke da shi kan batun Palastinu, watakila abun suke ciki yanzu ya ninka sau goma fiye da abin da ya faru tun farko; Maimakon ya zamo an manta da shi yana ma ƙara ƙarfi ne; haka siffar da ta kebenta ga aqida ta gama gari ta ke; Kuma tabbas hakan zai ci gaba.

Daidaitawa da gwamnatin Sahayoniya ita ce jan layin al'ummomi. Ba ruwana da gwamnatoci; domin suna wata irin Magana ne suna cewa. Idan kuka tambayi al'ummai, shin suna adawa da shi. Mafi yawan al'ummomi za kaga suna adawa da shi. Tabbas gwamnatin sahyoniya ma tana aikata laifuka, amma laifuka ba sa sanya cin nasara a kan kowa; Ta’addancin gwamnatin sahyoniyawa a Labanon, da ta’addancinta a Gaza ba, ko a yammacin gabar kogin Jordan da kungiyoyin Palastinawa ke gwagwarmaya awajen ba zai haifar masu da nasara ba; suna aikata laifukan ta’addanci da yawa a can, amma laifukan ta’addanci ba sa iya bada nasara ga wani. Wannan sunnah ce ta Ubangiji kuma a yau wannan abin tarihi yana faruwa a gaban idanunmu a Gaza da Lebanon.