Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta maku bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na Shahab cewa, an buga hotunan wasu fursunonin Palastinawa guda uku daga yankin Gaza da suka yi shahada a hannun yahudawan sahyuniya ‘yan sa’o’i kadan bayan an sako su.
A cewar shaidu, maharan sun yi musu luguden wuta ne daga jiragen ruwan yaki a kusa da birnin Gaza.



