10 Nuwamba 2024 - 11:26
Al-Sudani: Wayewar Tsayin Daka Da Gwagwarmaya Su Ne Suka Sanya Al'ummar Sudan Karkata Zuwa Ga Shi'anci.

Malam Muhammad Zaki Al-Sudani, dan Shi'a ne dan kasar Sudan, wanda ya yi karatu a makarantar hauza ta Qum, ya ce: Daya daga cikin batutuwan da suka sa mayar da dimbin al'ummar Sudan zuwa shi'anci, musamman ma masu ilimi; wayewar tsayin daka da gwagwarmaya wajen tunkarar kasashen yamma.


 

Malam Muhammad Zaki Al-Sudani A Wata Hira Da Ya Yi Da ABNA: Wayewar Tsayin Daka Da Gwagwarmaya Su Ne Suka Sanya Al'ummar Sudan Karkata Zuwa Ga Shi'anci.

Malam Muhammad Zaki Al-Sudani, dan Shi'a ne dan kasar Sudan, wanda ya yi karatu a makarantar hauza ta Qum, ya ce: Daya daga cikin batutuwan da suka sa mayar da dimbin al'ummar Sudan zuwa shi'anci, musamman ma masu ilimi; wayewar tsayin daka da gwagwarmaya wajen tunkarar kasashen yamma.

Kamfanin dillancin labaran kasa da aksa na Ahlul-Baiti (a.s) -ABNA- ya kawo tattaunawa ta musamman dangane da tarihin Shi’a kasar sudan wanda ya fara da cewa: Tarihin Shi'a a kasar Sudan ya samo asali ne tun zamanin daular Fatimiyawa, kuma sakamakon matsin lamba da Salahuddin Al-Ayyubi ya yi wasu daga sharifai da iyalan yan Shi'a sun yi hijira zuwa Sudan, kuma ana daukar cewa "Sadat Idris, da "Sadat Maragina," da "Sadat Arikiyyin sune asalin 'yan Shi'ar Sudan, kuma Sadat Al-Zaki su zuriyar Ishaq Al-Mutamin ne dan Imam As-Sadik da Sayyidah Nafisa (amincin Allah ya tabbata a gare su).

‘Yan shi’a Isna Ashariyya da ke a yau a Sudan su ne wadanda suka zama ‘yan Shi’a a cikin ‘yan shekarun da suka gabata suka koma ga Shi’arsu. Dukkan ‘yan Isna Ashriyya ‘yan asalin kasar Sudan ne, kuma akwai darikun Sufaye a kasar Sudan, musamman wasu daga cikinsu kamar Khatmiyyah da Ansar, wadanda suke da matukar kaunar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), kuma matsayin Imam Ali shi ne. mai girma a cikinsu.

A kasa akwai bayanin tattaunawar da aka yi da Malam Muhammad Zaki Al-Sudani dan Shi'a dan kasar Sudan wanda ya yi karatu a makarantar hauza ta Qum, dangane da yanayin 'yan Shi'ar Ahlul Baiti (a.s) a wannan kasa:

ABNA: Da Farko Dai Muna Bukatar Ka Ambaci Adadin Mutanen Sudan, Kuma Nawa Ne Adadin Musulmi Da ‘Yan Shi’a Mazauna Sudan?

Malam Muhammad Zaki Al-Sudani: Kasar Sudan tana arewa maso gabashin nahiyar Afirka, kuma tana da yawan mutane da ya kai miliyan 43 zuwa 44, kuma kashi 97 zuwa 98 cikin 100 musulmi ne, kuma 'yan Shi'a ne tsiraru, ba za mu iya ambata kaso nawa suke da shi ba, kamar yadda na sani, babu wani kididdiga a hukumance game da adadin 'yan Shi'a a Sudan, tabbas an yi bincike kan lamarin, amma babu cikakkiyar kididdiga, kuma duk da cewa an bayyana a cikin Atlas na 'yan Shi'a na duniya cewa, Sudan na da miliyan biyu ko uku na Shi'a, wannan abu ne zayyi wuya, kai tabbas ba ma gaskiya bane. Shekaru shida ko bakwai da suka gabata jami'an leken asirin Masar sun buga kidayar 'yan Shi'ar Sudan da Masar, kuma sun bayyana adadin ya kai 12,000, amma ba zan iya goyan bayan wannan adadin ba, kuma da alama adadin yayi kasa da haka.

Muna nufin ‘yan Shi’a Isna Ashariyya, da ke kan koyarwar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) a cikin aqidunsu da ayyukansu, idan kuma lamari ne da ya shafi soyayya ga Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) ko kuma da’awar zama ‘yan Shi’a kamar yadda wasu darikun Sufaye ke yi, to tabbas adadin ‘yan Shi’a ya zarce mutum miliyan 12. Mai yiyuwa ne Atlas na Shi'ar Duniya su ma sun dauki Masoya Ahlul Baiti Amincin Allah ya tabbata a gare su a matsayin ‘Yan Shi'ar Sudan.

ABNA: Shin Abubuwan Da Kuka Ambata Sun Hada Da Sudan Ta Kudu?

Ina nufin kasar Sudan, wadda sama da kashi 23 daga baya suka rabu da sunan "Sudan ta Kudu". Al'ummar Sudan ta Kudu yan asalin kabilun Afirka ne, kuma ta kunshi kabilun Nilotic Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu ne, ko dai ya zamo kiristoci sun fi musulmai yawa a Sudan ta Kudu ko kuma ya zamo adadinsu daidai da juna ya ke, wasu daga cikin mutanen Sudan ta Kudu ba su da addini, suna da nasu akida da kuma sihirce sihirce.

Ina nufin kasar Sudan da babban birninta, Khartoum, kafin ballewar Sudan ta Kudu, Khartoum ita ce cibiyar Sudan, kuma sunan Sudan shi ne "Jamhuriyar Sudan," kuma bangaren da ya rabu da ita ya kira kansa da kasa na "Sudan ta Kudu." Sunan Sudan shine "Jamhuriyar Sudan," kuma bangaren da ya rabu da ita ana kiransa da sunan kasar "Sudan ta Kudu".

ABNA: Za A Iya Cewa An Raba Sudan Da Yankin Mai Arzikin Man Fetur?

Idan kana an nufin yankin mai arzikin man fetur shi ne hakowarsa, eh, kusan kashi 70 cikin 100 na yankin mai arzikin man an raba shi da kasar Sudan, tabbas ban san hakikanin gwagwadonsa ba, amma galibin man da ake hakowa daga Sudan ta Kudu ne.

Abna: Kun Ambaci Cewa, Musulman Sudan Suna Son Ahlul-Baiti (Amincin Allah Ya Tabbata A Gare Su). Menene Alamun Wannan Soyayya A Sudan?

Musulunci a Sudan yana da dabi’ar Sufanci, abin da ake nufi da Sufaye ba shi ne (Ali Allah ne ba, wandanda suke Alantakar da Imam Ali) ba, a’a mutane ne ma’abuta dabi’a da ilimi, kuma galibin Sufaye ‘yan darikar Kadiriyya ne, kuma AbdulKadir Al-Jilani da Ma’arouf Al-Karkhi da Ibn Al-Arabi, ana daukarsu a matsayin shehunan darika a kasar Sudan, kuma mafiya yawan al’ummar Sudan ba su da wata soyayya ta musamman ga Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), yayin da Darikar Indiyawa ta yi imani cewa limamanmu tun daga Imam Ali (a.s) har zuwa Imam Al-Mahdi (AF), wato suna ganin imamai goma sha biyu ne imamansu, kuma mafi yawansu daga Sadat Al-Hasani da Al-Hussaini ne, Haka nan, kuma darikar “Marghaniyyah”. Itace darikar Khatmiyya daga Sadat Al-Hussaini, kuma sun yi imani da limamai Ahlul Baiti ne (amincin Allah ya tabbata a gare su), da cewa su ma’asumai ne, kuma a aqidarsu akwai alamar shi’anci.

Kuma dan shugaban ‘Khatmiyya Al-Marghaniyya’ da take darikar Sufaye ne a Sudan, sunansa Ja’afar Sadik, da sunaye kamar su Fatima, Ruqayya, Zainab, Kubra, Alawiyya, Mahbuba, Ummul-Hasan. Ummul-Husain, Ummul-Hasanain, Az-Zahra', Al-Batul, da dai sauran su a Sudan, wani lokacin kuma sai ka taras a cikin iyali guda takwas sunayensu Fatima ta wata siga. Misali a dangina sunan mahaifiyata Al-Batul, sunan kanwarta kuma Amina, Zainab, da Kubra, yayin da sunan Kakata ta wajen mahaifiyata Fatima ne, sunan yar uwar kakata Al-Zahraa, sunaye irin su Al-Baqir, Al-Sadiq da Jaafar suna da yawa a Sudan, kuma ba shakka, ya zama ruwan dare a Sudan ana kiran yara maza da sunan “Radi”. maimakon “Rida”, kuma sunaye irin su Al-Baqir, Al-Sadiq da Jaafar sun kebanta da ‘yan Shi’a, da sauran mazhabobi a kasar Sudan suna sanyawa ‘ya’yansu wadannan sunaye, kuma akwai sunaye masu yawa a Sudan Ali, Muhammad Husain, da Muhammad Hasan, kuma ga dukkan alamu na wanzuwar Shi'a ne.

Fatimiyyawan Masar wadanda ‘yan Shi’a ne a Sudan, sun yi tasiri sosai a Sudan, kuma sunaye irin su Karrar da Haider sunaye ne da suka kebanta da Shi’a, kuma sunan Aqeel ya zama ruwan dare a Sudan, kuma wannan lamarin yana nuni da shigowar Musulunci kamar yadda ya zo sakamakon son Ahlul-baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), amma kasar Sudan ta kasance kamar Alawiyyawa kasar Sham ta kasance mai nisa daga cibiyoyin ilmin Shi'a, kuma soyayya da sunayen Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) suna nan a cikin al'adun mutanen Sudan. Wasu sashen mazhabobin Sufaye sun anbata a cikin littattafansu sun ce ilimi da sani suna da hanyoyi guda biyu, na farko shi ne ilimin Shari'a, na biyu kuma shi ne ilimin gaskiya, kuma ilimin gaskiya yana zuwa ta hanyar wahayi zuwa daga Annbain Karshe (SAW) daga gare shi har zuwa Imam Ali (a.s), da Imam Hasan (a.s), da Imam Husaini (a.s), kuma bisa ga ra'ayin wasu wannan ilimi yana isowa ga sauran Imamai, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.

 

ABNA: Shin 'Yan Shi'ar Sudan Suna Da Husainiya Da Masallaci? Shin Suna Yin Tarukan Juyayi A Ranakun Al-Muharram, Musamman A Ranakun Tara Da Goman Sa?

Za a iya la'akari da lokuta biyu ga 'yan Shi'ar Sudan. A da can wasu ‘yan Shi’a da dama a Sudan sun yi imani da Shahada Uku, wasu suna kiransu da “Zabali’a” wasu kuma suna kiransu da “Batinun”. Kuma su fuskanci hare hare ne a lokacin Sallahaddin Al-Ayyubi da makamantansu. Shekaru dari da suka wuce, an yi ta fama da yaƙe-yaƙe da suka kai ga halaka waɗanda suka yin Shahadar Uku, ba shakka, alamunsu sun wanzu, musamman a yankunan arewa, wato mutanen arewa yankunan da ake kira Nubians, suna taron Ashura a cikin itatuwan dabino da kogin Nilu, suna kawo itacen dabino, suna kafa tantuna, suna kona su, mutane suna kuka suna dukan kansu. Amma wadannan ayyuka ba a hankalce sune yinsu ba, al'adu ne da abunda suka gada, kuma mutanen yankin ba sa kula da hakikaninsu har sai sun fahimci ma'anar abunda suke aikatawa. Tabbas wasu sun san cewa wadannan tarukan suna da alaka da Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) da Imam Husaini (a.s). Har yanzu al'adar tana nan kuma ta shuɗe a halin yanzu, amma shekaru 20 ko 25 da suka wuce abin ya zama ruwan dare.

Nau'i na biyu, a tarihi, su ne wadanda suka samu fahimtar Shi’a bayan nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran, kuma wadannan su ne 'yan Shi'a wadanda suke gudanar da tarukan makoki a lokacin Muharram, kuma hakan ya danganta ne da manufofin siyasar gwamnati na tuna a shekarun 1990s sun kasance suna halartar tarukan makoki a jami'o'i da wuraren taruwar jama'a, kuma 'yan Shi'a ba su da yawa kuma suna taruka na musamman a munasabobin Aimma (As) amma bayan haka, saboda zuwan 'yan Salafawa kasar, tunanin Umar Al-Bashir ga 'yan Shi'a ya canza, aka hana ayyuka da buga littafan Shi'a a Sudan. Don haka ayyukan ‘yan Shi’a sun takaitu ne ga wurare da gidaje iyaka, kuma gwamnatin Umar Al-Bashir ta kwace Shi’a Husainiyar Yan Shi’a.

ABNA: Shin 'Yan Shi'a Za Su Iya Bin Diddigin Lamarin Husainiyar Su Da Dawo Da Ita?

Na'am ana iya bibiyar lamarin a dawo da ita, amma mai kula Husainiyar yana iya da wani ra'ayi na daban, kuma na san cewa 'yan Shi'a a Sudan sun mayar da gidajensu wurin gudanar da ayyukan al'adu da addini, ko dai a cikin gidajensu ko kuma a wasu wurare kuma ana ci gaba da gudanar da ayyukan, kuma aikin karshe na ‘yan Shi’a a kasar Sudan shi ne a cikin watan Ramadan mai albarka a kwanakin shahadar Amirul Muminin (na raya layalul Qadar) kuma bayan wannan yaki ya barke, ban sani ba ko ‘yan Shi’a suna gudanar da ayyuka ne bayan yakin Khartoum, kai ina gani mayuwaci ne hakan ne saboda yanayin bai bayar da hakan ba kuma yana da hadari.

ABNA: Ina ‘Yan Shi’a Suka Bazu A Birnin Khartoum, Kuma A Wanne Yankuna Suka Fi Zama?

Yana daga abun sani cewa akwai ‘yan Shi’a da yawa a Khartoum; Domin kuwa babban birni ne, kuma ina tunanin akwai miliyan 10 ko sama da haka a cikinsa, kuma tabbas ‘yan Shi’a ana daukarsu a cikin al’umma, kuma ba su da yankinsu a birnin Khartoum. ‘yan Shi’a suna nan a ko’ina a cikin birnin, kuma a wasu yankunan sun fi yawa.

Tabbas akwai 'yan Shi'a a wasu jihohin, kamar Kordofan, Darfur, Sennar, Port Sudan a yankin gabas, Bandar Sudan, Kogin Nilu da wasu yankuna da dama a cikin kasar, kuma ba na tunanin akwai wani gari ko ma wani kauye mai girma a kasar Sudan wanda babu ‘yan Shi’a a cikinsa, duk da cewa ‘yan Shi’a kadan ne.

Abna: Ku Yi Mana batu Game Da Salafawa A Sudan

Ana daukar Salafawa a matsayin al’umma daga Musulmai, abin da ake nufi da Salafawa ba Wahabiyawa ba ne, sai dai suna daukar Salaf a matsayin hujja. A wani lokaci Salafiyya na nufin mutane da kungiyoyin da ke da alaka da Saudiyya da ra’ayoyin Wahabiyawa, a wani lokacin kuma ana nufin kungiyoyin da suke da bas u da wata alaka da Saudiyya, irin su Al-Qaeda da kungiyar da ke aiki irin ta Ikwanil Musulmin, da kuma wadanda suke da ra'ayin Salafiyya da Wahabiyawa kuma suke kiran kansu "Sururi".

‘Yan Salafiyya sun shigo Sudan ne kusan shekaru dari da suka gabata, kuma ayyukansu na da yawa kuma suna da tasiri, ba shakka, ba wai yana nufin cewa mutane ‘yan Salafawa ba ne, a’a, a daya bangaren kuma galibin mutane Sufaye ne, sun yi fice a harkokin tattalin arziki da kasuwanci a Sudan, kuma suna da rawar gani a ... Ayyukan al'adu a Sudan, musamman a rabi na biyu na gwamnatin Umar Al-Bashir, amma a farkon rabin mulkin Umar Al-Bashir Gwamnati, Dr. Turabi, shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi ta Sudan, bai amince da 'yan Salafawa ba, shi ne shugaban wasu 'yan uwa musulmi a Sudan, wadanda ba su amince da Salafawa ba, amma bayan rabuwar Dr. Turabi da 'yan uwa musulmi mutanen da suka kasance daga cikin Ikwanil muslimin a cikin gwamnati ikonsu suka zamo 'yan Salafiyya, kuma Salafawa suna da makarantu da masallatai kuma suna da ayyuka masu yawa.

ABNA: Shin Salafiyya Tana Da Makarantar Hauza Ta Ilimi A Sudan?

Haka ne, suna da makarantun ilimi, cibiyoyin addini, jami'a, koleji, da kuma wallafe-wallafen suna shiga cikin baje kolin, Watakila fiye da rabin masallatai a jihohin Khartoum 'yan Salafawa ne suka gina ko kuma suka sake gina su. kuma 'yan Salafiyya suna aiki sosai ‘Yan Salafiyya suna samun tallafin kudi sosai, yayin da suke buga littafai da rarrabawa kyauta suna gina dakunan karatu na masallatai a daidai lokacin da Sufaye ba su iya yin hakan, haka nan ma ‘yan Salafiyya suna da ayyuka masu yawa a fagen yada labarai da sauran su.

Duk da dimbin ayyukan da suke yi, Salafawa sun iya karkatar da ra'ayin jama'a, amma ba su da wani tasiri a cikin al'umma. Wannan ya faru ne saboda yadda tafarkinsu ya ke na rashin kunya da maganganun banza, kuma suna anbatar da shehunan Sufaye wadanda mutane ke girmama su da mummunan kalamai, wato al'umma ba ta zama Wahabiyawa ba, sai dai sun yi tasiri a kan ra'ayin jama'a da sanin makamar hankali. Don haka wasu Sufaye sun yi kamanceceniya da ‘yan Salafawa a tunani, amma ba ‘yan Salafiyya ba ne, ana iya cewa mutanen Sudan sun yi watsi da ayyukan ta’addanci da tashin hankali na Wahabiyawa.

Har ila yau, hukumar addini ta kasance a hannun 'yan Salafawa a shekarun baya-bayan nan a lokacin mulkin Umar Al-Bashir. Don haka, sun yi tasiri sosai a kafafen yada labarai, tashoshin gwamnati, da kula da jaridu da wallafe-wallafe. Don haka Salafawa sun sami babban tasiri saboda kudi da karfin da suke da shi, amma abin da za a iya gani shi ne, duk da cewa sun jawo dimbin jama'a zuwa ga Wahabiyawa, su ma sun yi kasa a gwiwa, misali ga kowane dubu mutane daya ne ya bar koyarwar Shi'a, amma a cikin kowane mutum goma, mutum shida ne suka bar akidar Wahabiyawa, su kuma matasan da suke jin maganganun Wahabiyawa a cikin masallatai da halartar taronsu, sun gane cewa manufar Wahabiyawa ita ce ba batun addini ba, amma burinsu shi ne kudi da tasiri, don haka suka bar su.