A wanann karon ma sojojin yahudawan sahyuniya sun yi ikirarin kashe shugaban majalisar zartarwar kungiyar Hizbullah Sayyid Hashim Safiyuddin a hukumance a wani hari da suka kai makonni uku da suka gabata.
Kamar yadda Kafar yada labarai ta Al-Arabiya mai alaka da Saudiyya ta yi ikirarin cewa; Kungiyar Hizbullah ta gano gawar Sayyid Hashim Safiyyuddin.
Wadannan da'awar ta sake tasowa yayin da Hizbullah ba ta tabbatar da labarin shahadarsa ba a hukunce zuwa yanzu.