14 Oktoba 2024 - 15:51
Hizbullah Ta Kai Hari Sama Da Garuruwan Yahudawa 182 / An Jiyo Ƙarar Fashewar Abubuwa Masu Ƙarfi A Haifa

Majiyoyin Labaran yahudawa sun ruwaito cewa an ji karar fashewar abubuwa masu karfi a Haifa bayan jin karar kararrawar gargadi a wannan yanki.

Majiyoyin Labaran yahudawa sun ruwaito cewa an ji karar fashewar abubuwa masu karfi a Haifa bayan jin karar kararrawar gargadi a wannan yanki.

Sannan an sake jin karar fashewar wasu abubuwa a yankin Karmel da ke kudancin Haifa.

A dai dai lokacin da wadannan fashe-fashe suke faruwa, an yi jin karar kararrawar hadari a Haifa, Al-Jalil, Acre da sauran yankunan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Sannan An jiyo ƙarar ƙararrawa a cikin garuruwa matsugunan Sahayoniya sama da 182

Wakilin Al-Mayadeen a Kudancin Lebanon sun ruwaito cewa An harba rokoki guda biyu daga Lebanon zuwa Tel Aviv. Wanda a karon farko kungiyar Hizbullah tai amfani da irin wannan makami mai linzami.

Kafafen yada labaran kasar sun ce kungiyar Hizbullah ta yi amfani da makami mai linzami wajen kai hari a birnin Tel Aviv.

An dakatar da tashin jirage a filin jirgin sama na Ben Gurion gaba daya bayan faruwar waɗannan hare-haren.