A Ranar ɗari uku da saba'in da
uku na yaƙin; Yahudawa suka kai Harin bam a "Al-Nusirat da Al-Buraij" inda suka
canja salon aiwatar da wanna ta’addanci ta hanya anfani da butum-butumin na’aurar
Bom masu fashewa
Wannan wani takaitaccen Rahoto na kwana ɗari uku da saba'in da uku na yaƙin Gaza (Jiya, Asabar, 12 ga Oktoba, 2024)
Yayin da ake ci gaba da yakin Gaza yayin da makiya yahudawan sahyoniya suka koma anfani da na’urorin butum butimi masu fashewa domin lalata gine-gine baya ga hare-hare ta sama da suke kaiwa.
Sojojin mamaya na ci gaba da kai hare-haren soji a arewacin Gaza tare da neman raba arewacin kasar da sauran yankunan Gaza. Tun kwanaki 9 da suka gabata ‘yan mamaya sun kakaba wa Jabalia, Beit Hanoun da kuma Beit Lahia kawanya mai tsanani, kuma burinsu shi ne su kori Falasdinawa su sanya su yin hijira bisa tsarin da aka fi sani da Janaral.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya sanar da cewa sojojin mamaya sun tsananta kashe-kashen jama'a a Jabalia da arewacin Gaza tare da hana kwashe gawarwakin shahidan da suka yi shahada a 'yan kwanakin nan.
Har ila yau, 'yan mamaya sun sanya shinge don raba arewacin Gaza da sauran yankunan, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka lalata gidaje da dama a sansanin Jabalia ta hanyar amfani da bama-bamai na butum butumi, wanda ya yi sanadiyar shahidai da dama da jikkatar wasu.
Majiyoyin Falasdinawa sun bayar da rahoton cewa, 'yan mamaya sun kai hari a yammacin sansanin Nusirat da ke tsakiyar Gaza.
Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a yankin Al-Mawasi da ke yammacin Rafah da ke kudancin Gaza har sau biyu. Hakazalika jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a garin "Bani Soheila" da ke gabashin Khan Yunis a kudancin Gaza.
Sojojin mamaya sun kuma kai hari kan sansanin El Buraij da ke tsakiyar Gaza.
Majiyoyin Falasdinawa sun yi nuni da lalata wasu gine-gine a yammacin Jabalia da kewayen yankin "Al Saftawi" da ke arewacin Gaza tare da bama-bamai butum butumi da jiragen sama.
Falasdinawa 11 ne suka yi shahada tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai a sansanonin al-Nusirat da Jabalia a Gaza a daren jiya. Majiyoyin asibiti sun ba da rahoton shahadar mutane bakwai da jikkata wani adadi a harin bam da aka kai a wani gida a sansanin Nusirat, da kuma shahadar Falasdinawa hudu da jikkatar wani adadi a harin bam din da aka kai a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza, sannan kuma sun yi nuni da cewa. ga tabarbarewar yanayin wasu daga cikin wadanda suka jikkata.