12 Oktoba 2024 - 07:44
Hizbullah Ta Kai Sabbin Gagaruman Hare-Hare A Haifa Da Kuma Golan Ta Hanyar Harba Makamai Mai Linzami A Masana'antar Kera Makamai.

Tun a safiyar yau Asabar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai hare-hare da makamai masu linzami kan wurare da sansanonin gwamnatin sahyoniyawan a yankunan Haifa da Golan na kasar Siriya da yahudawa suka mamaye da kuma wata masana'antar sarrafa abubuwa masu fashewa.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya habarto bisa nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IRNA bisa nakaltowa daga hedkwatar yada labaran yakin Hizbullah ta kasar Labanon, mayakan gwagwarmayar muslunci na kasar Labanon a cikin wata sanarwa da suka fitar a yau sun sanar da cewa, sun kai hari kan wata masana'antar sarrafa bama-bamai na gwamnatin sahyoniyawa a kudancin yankin Haifa da ke arewacin yankunan da aka mamaye.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, domin nuna goyon bayanta ga al'ummar Gaza da gwagwarmayar Palasdinawa da kare kasar Labanon da al'ummarta, da misalin karfe 01:00 na safiyar yau, ta kai hari kan taron da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka yi a wurin "Al -Jardah" cibiyar da take dauke da makamai masu linzami da yawa.

Hakazalika, da karfe 3:45 na safiyar yau, Hizbullah ta kai hari kan sansanin makiya yahudawan sahyoniya a yankin "Mailya" da hare-haren rokoki.

Har ila yau mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon sun sanar da cewa: ta harba wani makami mai linzami kan wata buldoza na gwamnatin sahyoniyawan da ke kokarin barin sansanin Ramya da karfe 3:50 na safiyar yau.

Sansanin "Zariit" na daga cikin sansanonin da kungiyar Hizbullah ta murkushe a safiyar yau.

Har ila yau kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar a cikin wasu bayanai daban-daban a yau cewa ta kai hari kan sansanonin Soma da Houma da ke yankin Golan na kasar Siriya da aka mamaya da makami mai linzami.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, a ranar 22 ga watan September ne sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka fara kai munanan hare-hare a yankuna daban daban na kudancin kasar Lebanon. A cewar rahoton na ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon, hare-haren na wannan gwamnati ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan shahidai tare da jikkata wasu dubbai.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ba ta yi shiru ba dangane da yadda ake kai wa fararen hula hari a wannan kasa; ta kai hare-hare da dama a kan matsugunan yahudawan sahyoniya a arewacin kasar Palastinu da aka mamaye, kuma a cikin kwanaki da sa'o'i da suka gabata, ta hanyar harba daruruwan rokoki, ta yi ruwan rokoki kan wuraren gwamnatin sahyoniyawan.